Wanda ake nema
Bayani wanda zai kawo hukunci…

Zulkarnaen

Tukuicin Da Ya Kai Na Dala Milyan 5

Zulkarmaen, wanda sunansa na asali shine Aris Sumarsono, wasu abokansa mayaka suna kiransa Daud. Jami’an Amurka da na Indonesia sunce Zulkarnaen ya zama shugaban gudanarwa na kungiyar Jemaah Islamiyah (JI) bayanda aka cafke mutumen da ake zargin cewa shine ya gada Riduan Isamuddin wanda kuma aka sani da lakabin Hambali.

Ana yi wa Zulkarnaen daukar kamar shine mutum mai mukami mafi girma a shugabancin kungiyar ‘yan ta’addar Jemaah Islamiyah dake nahiyar Kudu-maso-gabashin Asia. Ana kyautata zaton cewa shine yayi jagorancin kungiyar mayakan nan da suka kai harin kunar bakin wake akan Hotel din Marriott ta Jakarta inda aka aka kashe mutane 12 a shekarar 2003, kuma suka hada bama-bamman da aka yi anfani da su wajen kai hari a Bali a shekarar 2002 inda aka hallaka mutane 2002

Zulkarnaen daya ne daga cikin mutanen dake cudanayar kai tsaye da al-Qaida a nahiyar Kudu-maso-gabashin Asia. Zulkarnaen ya sami digiri a fannin halittu daga wata jami’a ta kasar Indonesia kuma, a shekarun 1980s, yana daya daga cikin ‘yan kasar Indonesia na farko da suka fara tafiya Afghanistan don karbar horo akan hanyoyin makirci da bata shirye-shirye. Yanzu haka kuma Zulkarnaen yana jagorantar wata rundunar mayaka da ake kira Lasker Khos ko “rundunar musamman” wacce mayakanta an samo su ne daga wasu daga cikin ‘yan kasar Indonesia 300 da suka sami horaswa a Afghanistan da Philippines.

Zulkarnean dalibi ne a karkashin Abdullah Sungkar, wanda ya kafakungiyar JI da wata makarantar zaman dalibbai da ake kira al-Mukmin inda aka koyarda Zulkarnean da sauran dalibban mayaka. A tsakiyar shekarun 1980s ne Sungkar ya aika wata kankanen gungu na ‘yan Indonesia zuwa Afghanistandon su sami horaswaa a sansanin kwamandan ‘yan Mujahidin, Abdul Rasul Sayyaf. Kafin rasuwar Sungkar a shekarar 1999, an sha ganin Zulkarnean a gefensa, yana taimakawa wajen shirya tarukka da kuma jadawalin aiyukkan da shi marigayin shugaban nasa zai aikata.

Ana kyautata zaton cewa Zulkarnean ya taimaka wajen shirya fadan da aka yi a tsibirran Maluku a shekarun 1990s, da kuma shirya tarukka a tsakanin mayakan da suka sami horaswa a kasar Afghanistan a lokutta daban-daban, abinda ya basu damar hada karfi wuri guda.