Wanda ake nema
Bayani wanda zai kawo hukunci…

Zerrin Sari

Tukuicin Da Ya Kai Na Dala Milyan 3

Zerrin Sari babbar kusa ce a kungiyar Juyin Juya Hali ta Turkiya (wacce a harshen Turkanci ake kira Devrimci Halk Kurtuluş Partisi Cephesi, ko DHKP/C). Kungiyar DHKP/C ta jima tana auna kadarorin Amurka har ma da sojoji, ma’aikatu da ma’aikatan soja da na diplomasiyar Amurka tun daga lokacinda aka kafa ta a 1994, lokacinda kungiyar da ta gada ta Devrimci ko Dev Sol ta wargaje zuwa kungiyoyi daban-daban. Manufarta dai itace ta goge duk wanta alama ta Amurka da NATO daga Turkiya, ta maye gurbinsu da kasa mai bin tafarkin kwaminisanci. A cikin watan Fabrairun 2013 ne wani dan kunar bakin wake da da alaka da kungiyar ya kai hari akan Opishin Jakadancin Amurka dake Ankara, har ya kashe wani dogari dan Turkiya.Tun shekarar 1997 Ma’aikatar Harakokin Wajen Amurka ta kaddamarda kungiyar DHKP/C a matsayin kungiyar ta’addanci, sannan ta sake nazarin wannan kuma ta sake sabunta shi a ran 24 ga watan Yulin 2013.

Zerrin Sari lauya ce da tayi aikin kare kungiyar Dev Sol a shekarun 1990s har zuwa lokacinda ta gudu, ta bar Turkiya a shekarar 1993. ita matar auren Dursun Karatas ce, wanda ya kafa kungiyar DHKP/C, kuma tare suka shata aiyukkan kungiyar a kasashen Turai. A shekarar 1999 ne aka gurfanarda Sari a gaban kotu a kjasar Belgium, har aka saka ta gidan kurkuku amma aka sake ta a shekarar 2008, shekrar da cutar sankara ta kashe mijinta Karatas. An kuma ce itace shugabar asiri ta DHKP/C kuma ma itace ta bada umurnin harin da aka kai akan hekkwatar ‘yansanda ta Turkiya da kuma rukunin gidajen ‘yansanda dake Ankara a ran 20 ga watan Satumbar 2013. Ance kuma Sari ce, tareda Musa Asoglu, suka sa aka kai farmakin nan na watan Maris na shekarar 2013 akan Ma’aikatar Shar’a ta Turkiya da kuma Jam’iyyar AKP.

Musa Asoglu, Zerrin Sari da Seher Demir duk manyan shugabanni ne na kungiyar Juyin Juya Hali ta Turkiya ta DHKP/C (wacce a harshen Turkanci ake kira:: Devrimci Halk Kurtuluş Partisi Cephesi, or DHKP/C).

Karin Hotuna

Karin Hoton Zerrin Sari
Karin Hoton Zerrin Sari