Wanda ake nema
Bayani wanda zai kawo hukunci…

Abu-Yusuf al-Muhajir

Tukuicin Da Ya Kai Na Dala Milyan 3

Abu Yusuf al-Muhajir gwanin hada bama-bamai ne. Shi tsohon dan kungiyar Tawhid w’al Jihad-Egypt (TWJ-Egypt) ne, wanda wata kungiyar masu matsanancin ra’ayi ce dake a yankin Duru-Sinina a tsakanin shekarun 2004-2006, wacce kuma ta aka sake fasalinta a shekarar 2011.

Ita dai kungiyar Tawhid w’al Jihad a masar wata gamayya ce ta ‘yan kasar Masar hade da mutanen kasashen ketare masu matsanancin ra’ayi da mazauninta yake a yankin Duru-Sinina wacce kuma ke rungumar akidar yin jihadi a duniya, wacce kuma ke auna mutane fararen hula da gwamnatocin da take jin basa bin ka’idodin Shari’ar Musulunci. TWJ ta jima tana alaka da sauran kungiyoyi da mutane masu matsanancin ra’ayi.

Abu-Yusuf na da hannu a cikin shirye-shiryen kai farmaki akan wasu mutane da kadarori na Amurka dake Masar, watakila ciki harda Opishin Jakadancin Amurka.