Wanda ake nema
Bayani wanda zai kawo hukunci…

Yasin Kilwe

Tukuicin Da Ya Kai Na Dala Milyan 3

Yasin Kilwe shine sarkin al-Shebaab a Puntland dake arewancin Somalia. A matsayinshi na shugaban mayakan Galgala Hills dake Tsaunukkan Golis, Kilwe ya bayyana biyayyarsa ga al-Shebaab da al-Qaida acikin wata sanarwa rubutacciya da aka karanta a wata tashar erdiyo da al-Shebaab ke jan ragamarta a wajajen karshen watan Fabrairun shekarar 2012. Sarkin al-Shebaab Ahmed Abdi aw-Godane ne da kansa, a hukumance, ya nada Kilwe a matsayin shugaban al-Shebaab na yankin. Shi dai Kilwe daga ‘yan asalin Dubays na Warsangali ya fito. An dade ana zarginsa da laifin shirya kai hare-hare da dama akan jami’an Puntland.

Al-Shabaab itace bangare mayaka na Majalisar Kotunan Somalia wacce ta kwace aksarin sassan kudancin Somalia a rabin karshe na shekarar 2006. Al-Shebaab ta ci gaba da gudanarda aiyukkanta na ta’addanci a sassan kudanci da tsakiyar Somalia. Kungiyar ta sha daukan alhakin kai hare-haren bama-bammai barkattai – cikinsu har da na kunar bakin wake – a Mogadishu da tsakiya da arewancin Somalia, inda dsau da yawa takan auna jami’an Gwamnatin Somalia da wadanda ake ganin kamar kawaye ne ga Gwamnatin Wucingadin (TFG) ta Somalia. Mai yiyuwa ne al-Shebaab ce ta kai wasu hare-hare guda biyar na kunar bakin wake da aka kai a watan Oktobar 2008 akan wasu birane biyu na arewancin Somalia, inda aka kashe mutane 26, aka raunana wasu 29. Haka kuma al-Shebaab ce ta kai tagwayen hare-haren kunar bakin wake a Kampalar Uganda a ran 11 ga watan Yulin 2010, inda mutane fiyeda 70 suyka hallaka, ciki harda Ba’Amurke daya. Wannan kungiyar ce ke da alhakin kashe ‘yan hankoron neman sauyi barkattai, ma’aikatan bada agaji, tarin manyan jagabannin jama’a fararen hula da ‘yanjarida. A cikin watan Febrairun 2012 ne al-Shebaab da al-Qaida suka bada sanarwar kulla kawance a tsakaninsu.

AA ran 26 ga watan Fabrairun 2008 ne Ma’aikatar Harakokin Waje Amurka ta kaddamarda al-Shebaab a matsayin Kungiyar Ta’addanci ta Kasashen Waje a karkashin Sashe na 219 na Dokar Shige da Fice da Zama Dan Kasa (kamar yadda aka gyara ta), da kuma kaddamarda da ita a matsayin Kungiyar Ta’addanci ta Musamman a karkashin Dokar Hukuma mai lamba 13224 ran 29 ga watan Fabrairu na 2008.