Wanda ake nema
Bayani wanda zai kawo hukunci…

Yasin al-Suri

Tukuicin Da Ya Kai Na Dala Milyan 10

Ezedin Abdel aziz Khalil, wanda aka fi sani da lakabin Yasin al-Suri, babban jigon al-Qaida ne dake zaune a Iran. A watan Disamban 2011 ne hukumomin Iran suka kame al-Suri bayanda aka bada sanarwar cewa Shirin Tukuici Don Adalci zai bada ladar Dala milyan 10, amma kuma yanzu ya koma yaci gaba da aikinsa na shugabancin reshen AQ na Iran.

A matsayinshi na mai jagorancin harakokin al-Qaida a Iran, aikin al-Suri ne shiriya kokarin al-Qaida na daukar kwararrun mayaka da jagabanni da sauran shugabanni, daga Pakistan zuwa Syria, da shirya hanyoyi da sababbin kurata zasu bi su isa Syria ta hanyar ratsa kasar Turkiyya, da kuma shirya tafiyar ‘yan al-Qaida masu aiki a waje don tabattarda ganin sun isa kasashen Yammacin Turai.

Al-Suri na daukar kudade da sababbin kuarata daga Yankin Gabas ta Tsakiya, yana kaiwa Iranm, daga nan zuwa Pakistan don baiwa manyan shugabannin al-Qaida karin karfin gwiwa. Hukumomin Iran na da wata alaka da al-Suri kuma sun kyale yana ci gaba da aiyukkansa a cikinkasarsu tun daga shekarar 2005.

Al Suri na samo wa al-Qaida kuratan mayaka daga kasashen Gulf zuwa Pakistan da Afghanistan ta hanyar Iran. Haka kuma shi hamshakin mai tarawa al-Qaaida kudade ne kuma ya sha samo mata dimbin kudade daga masu badatarbacce na dukkan kasashen Gulf. Al-Suri na anfani da hanyoyinsa na cikin Iran wajen aika mankudan kudade zuwa ga shugabannin al-Qaida dake Afghanistan da Iraq.

Ta hanyar aiki da gwamnatin Iran, al-Suri yakan samo hanyoyin ganin an sako ‘yan al-Qaida dake tsare a gidajen kurkukun kasar Iran. A duk lokacinda aka sako fursunonin al-Qaida, hukumomin Iran sukan hannunta su ga al-Suri wanda shi kuma zai nemi hanyar tura su Pakistan.

Karin Hotuna

Yasin al-Suri