Wanda ake nema
Bayani wanda zai kawo hukunci…

Yahya Haqqani

Tukuicin Da Ya Kai Na Dala Milyan 5

Yahya Haqqani babban jigo ne na Kungiyar Haqqani wanda ke da hannu dumu-dumu wajen harakokin yake-yake, kudade da kuma farfaganda na kungiyar. Yahya ya sha rike mukamin shugabancin kungiyar a duk lokacinda manyan shugabanninta irinsu Sirajuddin Haqqani (surukin Yahya din), Khalil Haqqani da Badruddin Haqqani (marigayi), basa nan. Haka kuma Yahya ya sha zama jigon shirya aiyukkan kungiyar Haqqani, ya kuma sha samarwa kwamandojinta kudade, cikinsu harda wani mukarrabin marigayi tsohon kwamandan mayakan Haqqani, Sangin Zadran da kuma shugaban tsara aiyukkan kungiyar Haqqani, Abdu Rauf Zakir. Sannan kuma Yahya ya taba aiki a maysayin mai yi wa Sirajuddin Haqqani fassarar Larabci da kuma masinja nashi.

Yahya yayi wa kungiyar aiyukka da yawa don tabattarda nasarar hare-hare da sauran aiyukkan da kungiyar Haqqani ke gudanarwa. A farkon shekarar 2013 ne ya shirya bude asusuna da yawa don samarwa mayakan Haqqani kudade. Har ila yau a cikin wannan shekara ta 2013 ne ya shirya daukar kayan aiki daga Haddadiyar Daular Larabawa zuwa wajen shugaban kungiyar Haqqani, Khalil Haqqani. Sannan a shekarar 2012 Khalil ya tsara aikin rarraba nakiyoyin IEDs da kayan aiyukkan sadarwa, sannan kuma yayi nazarin dabarun da aka shata na kai harin da kungiyar Haqqani ta shiryawa kaiwa a ran 7 ga watan Agustar 2012 akan Barikin “Forward Base” a lardin Logar na Afghanistan wanda a cikinsa aka raunana mutane goma-sha-uku, ciki harda fararen hula goma sha daya ‘yan Afghanistan. A cikin shekarar 2011 Yahya yayi aikin daukar kudade daga Sirajuddin Haqqani, yana rarrabawa kwamandojin Kungiyar Haqqani don gudanarda aiyukkansu.

Wani lokaci Yahya yakan zama mai shiga-tsakani a tsakanin kungiyoyin Haqqani da na al-Qaida, kuma tun akalla tsakiyar shekarar 2009 yake da dangantaka da al-Qaida. A wannan matsayin, aikin Yahya ne ya rinka rarraba wa ‘yan al-Qaida kudade don harakokin kansu na kansu. Haka kuma a tsakiyar shekarar 2009, yayi zama mai cudanya da sunan Kungiyar Haqqani da mayakan kasashen ketare da suka hada da Larabawa, Uzbikawa da ‘yan Chechnya.

Haka kuma Yahya ne yayi jagorancin harakokin watsa labarai da cudanya da kafafen watsa labarai da sunan kungiyoyin Haqqani da na Taliban. Tun farkon shekarar 2012 Yahya yakan hadu da Sirajuddin don nema sa-albarkacin bakinsa akan fayafayin bidio na farfaganda na Taliban da shi Yahya ya shirya. Tun akalla shekarar 2009 Yahya yake aiki kan harakokin watsa labaran Haqqani, lokacinda yake gyara fayafayen bidiyo da ake samowa daga mayakan dake Afghanistan, inda ya rinka aiki a wani situdiyo dake a wata makaranta ta Haqqani. Har zuwa karshen shekarar 2011, Yahya yana samo kudaden watsa labaran ne daga Sirajuddin Haqqani ko kuma wani mukarrabi na shi Sirajuddin din.

A ran 5 ga watan Fabrariun 2014 ne Ma’aikatar Harakokin Wajen Amurka ta kaddamarda Yahya Haqqani a matsayin Rikakken Dan Ta’adda na Duniya a karkashin Dokar Hukuma mai lamba 13224.

Karin Hotuna

Karin Hoton Yahya Haqqani
Karin Hoton Yahya Haqqani