Aikin Ta’addanci
Bayani akan ...

Harin Bam akkan Cibiyar Ciniki ta Duniya

New York City | 26 ga Fabrairu, 1993

A ran 26 ga watan Fabrairun 1993 ne wani bam na cikin mota ya tashi a karkashin Ginin Farko na Cibiyar Ciniki ta Duniya dake birnin New York. Manufar da aka so cimma da kai wannan harin da bam mai nayin Laba 1,500 shine a ruguza dukkan manyan tagwayen gine-ginen guda biyu ta hanyar ingiza Ginin Farko akan Gini na Biyu, don hallaka dubban mutane. Koda yake bam din bai lahanta ko daya daga cikin gine-ginen biyu ba, ya janyo mutuwar mutane biyu, dubbai sun ji raunukka, ya kuma haddasa barnar milyoyin daloli.

Wasu dake da alaka da kungiyar al-Qaida da suka hada da Abdul Rahman Yasin, Ramzi Yousef da sauran mutane da dama ne suka shata kai wannan farmakin. Khalid Shiekh Mohammed, kawun ramzi Yousef kuma daya daga cikin manyan shugabannin al-Qaida shine ya samarda kudaden kai wannan harin. Tuni aka yanke hukunci akan shidda daga cikin wadanda ke da hannu a kai wannan harin, cikinsu harda madugunsu Ramzi Yousef.

Shirin Bada Tukuici Don Adalci na tayin bada tukuicin da ya kai har na Dala milyan 5 ga duk wanda ya bada bayanin da zai kai ga kama wadanda suka kai wannan harin.