Aikin Ta’addanci
Bayani akan ...

Hari akan Jirgin Ruwan USS Cole

Aden, Yamal | 12 ga Oktoba, 2000

A ran 12 ga watan Oktobar 2000 ne wasu ‘yan kunar bakin wake su biyu suka shake jirginsu na kwale-kwale da nakiyoyi kuma suka rabka shi akan Jirgin Ruwan USS Cole na Amurka a lokacinda yake tsaye a tashar jiragen ruwan Aden, Yamal. Wannan ya haifarda wani katon rame a jikin jirgin ya kuma hallaka sojojin ruwa 17, ya raunana wasu sunfi 30. ‘Yan al’Qaidan da suka shirya kai wannan farmakin sun hada da Jamal Mohammad al-Badawi da Fahd Mohammed Ahmed al-Quso.

Shirin Bada Tukuici Don Adalci na tayin bada tukuicin da ya kai har na Dala milyan 5 ga duk wanda ya bada bayanin da zai kai ga kama wadanda suka kai wannan harin.