Aikin Ta’addanci
Bayani akan ...

Harin Bam akan Kulob din USO

Naples, Italiya | 14 ga Afrilu, 1988

A ran 14 ga vwatan Afrilun 1988 ne, wani bam ya tashi daga cikin wata mota a gaban Kulob na USO dake birnin Naples, Italiya. Farmakin ya hallaka jimillar mutane biyar da suka hada da wata sojar Amurka macce daya, ya kuma raunana mutane 15, cikinsu harda sojan Amurka hudu.. A ran 9 ga watan Afrilun 1993 aka chaji Junzo Okudaira, wani dan kungiyar ta’addanci ta Jajayen Sojan Japan (JRA) da laifin kai wannan ahrin na Naples. Haka kuma shi Okudaira ne ake tuhuma da laifin kai harin bam din mota da aka kai a kan Opishin jakadancin Amurka dake Rome a cikin watan Yunin 1987.

A cikin shekarar 1970 aka kafa kungiyar JRA bayanda ta balle daga cikin bangaren Rundunar Jajayen Sojan Kwaminis na Japan. A lokacinda take cikin hayyacinta, kungiyar nada membobi sun kai 40 kuma ana mata daukar daya daga cikin kungiyoyi mafi zama cikin shirin fada a duk duniya. A cikin shekarun 1970s, kungiyar JRA ta sha kai hare-haren a sassan duniya daban-daban ciki harda harin da aka kai kan filin jirgin saman Lod na Isra’ila a shekarar 1972, da sace wasu manyan jiragen saman japan guda biyu da kuma yunkurin kama Opishin Jakadancin Amurka dake Kuala Lumpur.

Babban makasudin kafa JRA tun asali shine don tumbuke gwamnatin japan da Gidan sarauta na kasar; sai dai kuma an cafke madugun kungiyar a shekarar 2000 wanda yassa shekara guda bayan hakan, kungiyar ta wargaje. Ganin irin tarihi zumuncin kut da kut dake tsakanin kungiyar da kuma kungiyoyin ta’addancin Palesdinawa yassa wasu suka zaci cewa kungiyar JRA din ta tashi, ta maida mazauninta a yankin Gabas ta Tsakiya.

Shirin Bada Tukuici Don Adalci na tayin bada tukuicin da ya kai har na Dala milyan 5 ga duk wanda ya bada bayanin da zai kai ga kama wadanda suka kai wannan harin.