Aikin Ta’addanci
Bayani akan ...

Hari Akan Opishin Jkaadancin Amurka

Athens, Grka | 12 ga Janairu, 2007

A ran 12 ga watan Janairun 2007 ne, wani rokan gurneti ya abka kan Opishin Jakadancin Amurka dake Athens. Kungiyar da ta dauki alhakin kai harin mai suna “Revolutionery Struggle” ana jin wani reshe ne na kungiyar ‘yan ta’adda ta kasar Grka mai suna “November 17”.

Kungiyar “November 17” ce ke da alhakin tarin hare-haren da aka jima ana kaiwa a kasar grka tun daga shekarun 1970s da suka hada da harbe-harbe, hare-haren rokoki da bama-baman motoci. Wannan ta’addancin nasu ya janyoi mutuwar Amurkawa hudu: Richard Welch, George Tsantes, William Nordeen da kuma Ronald Stewart.

Shirin Bada Tukuici Don Adalci na tayin bada tukuicin da ya kai har na Dala milyan 1 ga duk wanda ya bada bayanin da zai kai ga kama wadanda suka kai wannan harin.