Aikin Ta’addanci
Bayani akan ...

Hare-haren da aka tsara ko wadanda aka riga aka kai akan Ma’aikatun Diplomasiya na Amurka a Duniya baki daya

Shirin Tukuici Don Adalci na tayi bada goron da zai iya kaiwa na Dala milyan 3 ga duk wanda ya bada bayanin da zai sa a yi rigakafi ko kuma a shawo kan duk wani harin ta’addancin da aka shirya kaiwa akan duk wani Ba’Amurke ko kadarorin dake da alaka da duk wani Opishin Diplomasiyar Amurka. Duk wanda ya bada bayanin dake da alaka da shirin kai hari ko wasu hare-hare na can baya da aka kai kan opisoshin jakadancin, zai iya samun wannan tukuici. Ma’aikatun Diplomasiyar Amurka sun hada da opisoshin jakadancin, kananan opisoshin jakadanci, opisoshin bada biza, rassan opisoshin jakadu da duk sauran ma’aikatun wakilci a ko ina a duniya.