Labarin kan nasara

Uday Hussein

Marigayi

Uday Hussein shine babba a cikin ‘ya’yan Saddam maza guda biyu da ya haifa daga aurensa na farko kuma shi Uday yayi kaurin suna saboda rashin imaninsa da halinsa na rashin tabbas. A matsayinsa na shugaban Kwamitin Wassanin Olympics, yak an bada umurnin a azabtarda ‘yanwasan da basu yi abinda zai burge shi ba. Shi da kansa yana da hannu a cikin kisan gillar da aka yi wa surukansa biyu maza‘yanuwan matarsa.

Bayanin da wani sheda ya bada a ran 23 ga watan Yulin 2003 ne ya kai ga a gano inda Uday da Qusay Hussein suke. Tareda taimakon Bataliyar mayakan Sama ta 101 ne rundunar soja ta 20 ta kai samamen kama wadanan mutanen. An gwabza yaki na sa’oi hudu wanda ya zama sanadin a kashe Uday da Qusay Hussein.