Aikin Ta’addanci
Bayani akan ...

Ace Jirgin Saman TWA mai lamba 847

Beirut, Lebanon | 14 ga watan Yuni, 1985

A ran 14 ga watan Yunin 1985 wasu ‘yan ta’adda masu alaka da Hizbollah suka sace jirgin saman kampanin TWA mai lamba 847 dake kan hanyarsa daga Athens ta kasar Grka zuwa birnin Rome na Italiya. ‘Yan ta’addar sun juya alkiblar jirgin zuwa Beirut, Lebanon inda suka yi musayar wasu daga cikin pasinjojin, aka basu man jirgin. Daga nan jirgin ya tashi zuwa Algiers, Algeria inda suka kara sakin karin pasinjoji kafin kuma su sake komawa Beirut.

A Beirut ne kuma ‘yan ta’addar suka tantance gwanin ninkaya, Sojan Ruwan Amurka Robert Stethem. ‘Yan ta’addar sun yi wa Stethem duka, suka harbe shi kana suka yada gawarsa akan fakon filin jirgin sama. A Beirut, karin mutane 12 dake dauke da makamai suka shiga jirgin wanda wanda ya koma Algiers inda nan ma aka kara sakin pasinjoji 65.

Karshenta dai jirgin ya sake komawa Bierut inda ya zauna har zuwa ranar 30 ga watan Yuni wanda lokacin ne aka saka sauran pasinjojin cikin mota, aka tuka su zuwa Syria. A can Syria an saka su cikin wani jirgin Rundunar Sojan sama ta Amurka, aka kai su Jamus. ‘Yan ta’addar da suka cinna wannan ta’asar sun hada da Ali Atwa, Hassan Izz-al-Din, Mohammed Ali Hamadei da sauran wasu da dama.

Shirin Bada Tukuici Don Adalci na tayin bada tukuicin da ya kai har na Dala milyan 5 ga duk wanda ya bada bayanin da zai kai ga kama wadanda suka kai wannan harin.