Aikin Ta’addanci
Bayani akan ...

Harin Bam kan Jirgin Saman TWA mai lamba 840

Grka | 2 ga Afrilu, 1986

A ran 2 ga watan Afrilun 1986 ne wani bam ya fashe a cikin jirgin ssaman kampanin TWA mai lamba 840 yayinda yake tafiya daga Rome, Italiya zuwa Athens, GRka. Wannan fashewar ta jiho wasu Amurkawa hudu dake cikin jirgin zuwa waje, kuma cikinsu ba wanda ya tsira da ransa. Daga cikin mutanen hudu harda wata ‘yar jaririya mai wattani 9 da haihuwa da kuma mahaifiyarta. Akwai kuma wasu pasinjoji biyar da suka ji rauni saboda sukewar iska a cikin irgin. Sauran matafiya 110 dake cikin jirgin duk sun tsra bada jin rauni ba.

Shirin Bada Tukuici Don Adalci na tayin bada tukuicin da ya kai har na Dala milyan 5 ga duk wanda ya bada bayanin da zai kai ga kama wadanda suka kai wannan harin.