Aikin Ta’addanci
Bayani akan ...

Fasa-Kwabrin Kayan Tarihi da na Mai dake anfanar Kungiyar Islama ta Iraq da Levant (ISIL)

Shirin Bada Tukuici Don Adalci na tayin bada ladar da zata kai har Dala milyan 5 ga duk wanda ya bada bayanin da zai kai ga tsaida saye ko sayarda mai da kayan tarihi da ake don anfani, ko da sunan, ko a madadin kungiyar ‘yan ta’addar nan ta ‘yan kishin Islama (ISIL) ta Iraq da Levant wacce kuma aka sani da lakabinta na Larabci, watau DAESH.

Kungiyoyin ‘yan ta’ada irinsu ISIL sukan dogara ne akan kudade da tallafin da suke samu wajen iya ci gaba da gudanarda aiyukkansu da kai hare-hare. Hanyoyin haramun da ISIL ke bi wajen sarrafawa da fasa-kwabrin hajojin mai da kayan tarihin da suke satowa daga kasashen Syria da Iraq na bude musu kafofin samun mankudan kudaden shiga, inda suke samun milyoyin daloli da kuma baiwa wannan hinjarrariyar kungiyar ta’addanci ta ISIL sukunin iya ci gaba da kai hare-harenta akan mutanen ba su san hawa ba, balle sauka. Akidar ISIL ta satar kayan tarihi daga kasashen Iraq da Syria ta janyo asara mai tarin yawa na kayan tarihi masu daraja na tsofaffin zamunnan da suka shige, wadanda kuma ba za’a iya sake maye gurbinsu ba. Tsofaffin kayan tarihi da suka hada da sulallan karfe, kayan alatu na dauarawa a wuya da hannu da duwatsun lu’lu’u, alluna, gumakai, masakai da allunan rubuce-rubuce na daga cikin dimbin kayan tarihi masu daraja na kasashen Syria da Iraq da kungiyar ISIL ke nema ruwa-a-jallo. Jan Littafen Jerin Gaggawa na Kayan Tarihi da Al’adu Masu Daraja Dake Fuskantar Hatsari, wanda Cibiyar Gamayyar GidajenTarihi ta Kasa da Kasa ta hada tareda tallafin Ma’aikatar Harakokin Wajen Amurka, na nuna cikakken bayani na irin kayan da aka sato da kuma ana fasa-kwabrinsu daga Syria da Iraq, kuma aka hade su http://icom.museum/resources/red-lists-database/red-list/syria/ da http://icom.museum/resources/red-lists-database/red-list/iraq-2015/.

Ma’aikatar Harakokin Wajen Amurka, wacce ke da burin tsinke duk wasu hanyoyin samun kudi na kungiyar ISIL, na fatar cewa wannan tayin na bada tukuci zai taimaka wajen gano mutane ko cibiyoyin da ke taka rawa wajen samarwa, bude hanyoyi, sarrafawa, fasa-kwabrin, rabawa, sayarwa ko cinikin hajojin mai ko kayan tarihi don anfanin ISIL, da kuma samarda bayanai akan kungiyoyin simoga, matakai da duk wasu hanyoyin da ake bi wajen gudanarda wadanan aiyukkan na assha.

http://eca.state.gov/video/conflict-antiquities-panel-1-video

http://eca.state.gov/video/conflict-antiquities-panel-2-video

Fasa-Kwabrin Kayan Tarihi da na Mai dake anfanar Kungiyar Islama ta Iraq da Levant (ISIL)

Hoton Fasa-Kwabrin Kayan Tarihi da na Mai dake anfanar Kungiyar Islama ta Iraq da Levant (ISIL)