Labarin kan nasara

Toting Craft Hanno

Wanda aka yanke wa hukunci

Toting Craft Hanno dan Kungiyar Abu Sayyaf ne da ke da hannu a cikin satar mutanmen da aka yi a 2001 na Dos Palmas.

A ran 27 ga watan Mayun 2001 ne kungiyar ASG ta sace wasu Amurkawa guda ukku daga wurin shakatawa na Dos Palmas dake aPalawan a kasar Philippines. Sunayen wadanan Amurkawan sune Guillermo Sobero da Martin da kuma Gracia Burnham, wadanda mishan ne na Amurka mata da miji. A ran 11 ga watan Yunin 2001 ne kakakin ASG, Abu Sabaya ya bada sanarwar cewa yasa an kashe Sobero a matsayin “kyautar taya murnar ranar haihuwa” ga shugabar kasar Philippines, Gloria Macapagal-Arroyo. A ran 7 ga watan Oktobar 2001 ne kuma aka tsinto wani kan bil adama da aka tantance cewa na Guillermo Sobero ne. A cuikin watan Yunin 2002 Martin Bumham ya rasa ransa a cikin fadan da aka gwabza tsakanin sojojin Philippines da mayakan ASG; An ji wa Gracia Bumham amma an ceto shi kuma aka maida shi Amurka.

An biya tukuicin Dala 100,000 ga wadanda suka bada labarin da ya kai ga kama Hanno a ran 6 ga watan Janairun 2005.