Aikin Ta’addanci
Bayani akan ...

Kashe-kashen Kampanin Petur na Union Texas

Karachi, Pakistan| 12 ga Nuwamba, 1997

A safiyar 12 ga watan Nuwamban 1997 ne wasu ma’aikata na kampanin fetur na Union Texas Petroleum suka fito zasu je aiki a Karachi ta Pakistan. A daidai lokacinda motarfsu ta tsallaka kan gada ne wasu ‘yan bindiga su biyu suka fito daga cikin motarsu, wata jar Honda Civic, suka soma harbin motar ma’aikatan. Dukkan ma’aikatan hudu Amurkawa hade da direbansu dan Pakistan, an kashe su nan take a cikin farmakin.

Masu lura da al’amurra da dama na daukar wannan harin a matsayin ramuwar gayya akan hukuncin da aka yanke wa Aimal Kansi koda yake, a hukunce, har yanzu ba’a tabattarda gaskiyar wannan zaton ba. An yanke wa Kansi hukunci akan kisan da aka yi a shekarar 11993 na ma’aikatan CIA guda biyu a bakin kofar Helkwatar hukumar dake Langley, jihar Virginia.

Shirin Bada Tukuici Don Adalci na tayin bada tukuicin da ya kai har na Dala milyan 5 ga duk wanda ya bada bayanin da zai kai ga kama wadanda suka kai wannan harin.

Wadanda abin ya shafa

Hoton Ephrahim Egbu
Ephrahim Egbu
Hoton William Jennings
William Jennings
Hoton Tracy Ritchie
Tracy Ritchie
Hoton Joel Enlow
Joel Enlow