Aikin Ta’addanci
Bayani akan ...

Sace Kevin Scott Sutay

El Retorno, Colombia | 20 ga watan Yuni, 2013

A ran 20 ga watan Yunin shekarar 2013 ne, Kungiyar ‘Yan Fafatikar Juyin-Juya Hali ta FARC ta Colombia suka sace Ba’Amurke Kevin Scott Sutay a garin El Retorno dake kasar Colombia. Shi dai Sutay, wanda tsohon sojan Amurka ne, ya jima yana tattakin tafiya a kasa a matsayin dan yawon bude ido inda ya ratsa kasashe da dama na nahiyoyin Tsakiya da Kudancin Amurka.

A ran 19 ga watan Yulin shekarar 2013 ne kungiyar ta FARC ta fito da wata sanarwa inda take daukan alhakin sace Sutay da kuma bayyana niyarta na sako shi don ta nuna cewa ita mai cika alkawari ce. Sai dai kuma ba’a sako Sutay ba sai ran 27 ga watan Oktobar shekarar 2013, lokacinda aka maida shi a hannun Ma’aikatar Guaviare , su kuma suka mika shi ga gwamnatocin kasashen Colombia, Cuba da Norway da kuma wakilan Kungiyar Bada Agaji ta Red Cross. Daga can ne aka hannunta Sutay ga jami’an gwamnatin Amurka dake Bogota, Colombia wadanda suka saka shi a jirgin sama, suka maida shi Amurka.

Shirin Bada Tukuici Don Adalci na tayin bada goron Dala milyan 3 ga duk wanda ya bada bayanin da zai ga a kama wadanda suka kai wannan harin.