Wanda ake nema
Bayani wanda zai kawo hukunci…

Sirajuddin Haqqani

Tukuicin Da Ya Kai Na Dala Milyan 10

A halin yanzu dai Sirajuddin Haqqani ne ke jagorancin aiyukkan yau da kullum na Kungiyar Haqqani. A cikin tadin da yayi da wata kafar watsa labarai ta Amurka, Sirajuddin ya amsa cewa shine ya tsara farmakin da aka kai ran 14 ga watan Janairun 2008 akan otel din Serena dake Kabul wanda ya hallaka mutane shidda, ciki harda Ba’Amurke Thor David Hesla.

Haka kuma Sirajuddin ya amsa cewa shine ya tsara yunkurin da aka yi a watan Afrilun 2008 na kashe shugaban Afghanistan Hamid Karzai. Ya kuma sha taka rawa a cikin hare-haren da akan kai kan iyaka akan sojojin Amurka da na Kawancen Kasashen Duniya dake a Afghanistan. Ana kyautata zaton yana zaune a cikin Yankunan Kabilun nan mallakar Gwamnatin Tarayyar Pakistan.

A cikin watan Maris na shekarar 2008 ne Ma’aikatar Harakokin Wajen Amurka ta kaddamarda Sirajuddin Haqqani a matsayin Rikakken Dan Ta’adda na Duniya a karkashin Dokar Hukuma mai lamba 13224.

Karin Hotuna

Karin Hoton Sirajuddin Haqqani
Karin Hoton Sirajuddin Haqqani