Aikin Ta’addanci
Bayani akan ...

Hare-Hare akan Cibiyar Ciniki ta Duniya da Ma'aikatar Tsaro ta Pentagon

11 ga Satumba, 2001

A safiyar 11 ga watan Satumbar 2001 ne wasu ‘yan ta’adda masu alaka da kungiyar al-Qaida suka kame wasu jiragen sama hudu na pasinja. Dukkan wadanan jiragen suna kan hanyarsu ne zuwa jihar california bayan da suka taso daga filayen jiragen sama daban-daban dake gabashin Amurka.

Jiragen sama biyu na farko da suka taso daga filin jirgin saman Logan dake Boaton, an sace su ne, sannan aka rabka su akan manyan Tagwayen gine-ginen Cibiyar Ciniki ta Duniya dake New York. Gaunin abkawar jiragen da kuma gagarumar gobarar da ta tashi a sabili da man jiragen, sun taru sun nakasa gine0ginen har ma karshenta suka roshe.

Jirgi na ukku da ya taso daga filin jirgin saman Dulles, shima an sace shi kana aka rabka shi akan ma’aikatar tsaron Pentagon, rabin awa bayan farmaki na biyu da aka kai akan Cibiyar Ciniki ta Duniya. Wannan harin yayi mummunan lahani ga ginin, ya hallaka dukkan mutanen dake cikin jirgin da kuma karin mutane 125 dake cikin ginin ma’aikatar.

Jirgi na hudu da ya taso daga filin jirgin saman Newark watakila an so yin anfani da shine wajen kai hari akan Majalisar Dokokin Amurka ta “Capitol” ko kuma Fadar Shugaban Amurka ta “White House.”. Sai dai kuma pasinjojin dake cikin jirgin sun kalubalanci ‘yan taa’ddar. Saboda jaruntakar wadanan pasinjojin, ‘yan ta’addan sun kasa cimma biyan bukatarsu kuma karshenta jirgin ya fadi a kusa da Shanksville, inda dukkan mutane 40 dake cikinsa suka hallaka.

Hare-haren da aka kai ran 11 ga watan Satumbar 2001 sun kashe jimillar mutane 2,998 da suka fito daga kasashen duniya dab an-daban. Kungiyar al-Qaida ta sa kai ta dauki alhakkin shiryawa da kai wadanan hare-haren kamar yadda shugabansu marigayi Usama Bin Ladin ya fada a wani sakon bidiyo da aka sako bayan kai farmakin. Wadannan sune hare-hare mafi muni da aka taba kawowa Aurka daga waje tun bayan wadanda aka kai akan Tashar Jiragen Ruwan Pearl Harbor a shekarar 1941.

Shirin Bada Tukuici Don Adalci na tayin bada tukuicin da ya kai har na Dala milyan 25 ga duk wanda ya bada bayanin da zai kai ga kama wadanda suka kai wannan harin.