Wanda ake nema
Bayani wanda zai kawo hukunci…

Seher Demir Sen

Tukuicin Da Ya Kai Na Dala Milyan 3

Seher Demir babban jigo ne na kungiyar Juyin Juya Hali ta Turkiya (wacce a harshen Turkanci ake kira Devrimci Halk Kurtuluş Partisi Cephesi, ko DHKP/C). Kungiyar DHKP/C ta jima tana auna kadarorin Amurka har ma da sojoji, ma’aikatu da ma’aikatan soja da na diplomasiyar Amurka tun daga lokacinda aka kafa ta a 1994, lokacinda kungiyar da ta gada ta Devrimci ko Dev Sol ta wargaje zuwa kungiyoyi daban-daban. Manufarta dai itace ta goge duk wanta alama ta Amurka da NATO daga Turkiya, ta maye gurbinsu da kasa mai bin tafarkin kwaminisanci. A cikin watan Fabrairun 2013 ne wani dan kunar bakin wake da da alaka da kungiyar ya kai hari akan Opishin Jakadancin Amurka dake Ankara, har ya kashe wani dogari dan Turkiya.Tun shekarar 1997 Ma’aikatar Harakokin Wajen Amurka ta kaddamarda kungiyar DHKP/C a matsayin kungiyar ta’addanci, sannan ta sake nazarin wannan kuma ta sake sabunta shi a ran 24 ga watan Yulin 2013.

A cikin shekarar 1980 Sen ta shiga kungiyar Dev Sol ta kuma taka rawa a cikin aiyukkan Dev Sol har zuwa 1994, lokacinda ta shiga cikin kungiyar DHKP/C inda kuma ta samu ci gaba a mukamai a Grka. An bada rahoton cewa ta kai ga zama shugabar reshen KHDP/C a birnin Athens. Ita wakiliya ce a Majalisar Zartaswa ta DHKP/C, wacce itace wuka da namar yanke hukunci akan aiyukkan kungiyar.

Musa Asoglu, Zerrin Sari da Seher Demir duk manyan shugabanni ne na kungiyar Juyin Juya Hali ta Turkiya ta DHKP/C (wacce a harshen Turkanci ake kira:: Devrimci Halk Kurtuluş Partisi Cephesi, or DHKP/C).

Karin Hotuna

Seher Demir Sen