Wanda ake nema
Bayani wanda zai kawo hukunci…

Sami Jasim Muhammad al-Jaburi

Tukuicin Da Ya Kai Na Dala Milyan 5

Sami Jasim Muhammad al-Jaburi, wanda kuma ake kira Hajji Hamid, jigo ne a ƙungiyar Daular Musulunci a Iraƙi da Syria (ISIS) kuma babban mamban kungiyar al- Ƙa’ida a Iraƙi wacce ta gabaci ISIS (AQI). Muhammad al-Jaburi ya taka rawa ga tafiyar da kuɗaɗen ayyukan ta’addanci na ISIS.

A yayin da yake matsayin mataimakin ISIS a kudancin Mosul a 2014, an bayar da rahotannin cewa matsayinsa tamkar na ministan kuɗi ne, inda yake kula da kuɗaɗen shiga na ƙungiyar daga man da take sayarwa da Gas da kuma ma’adinai ta ɓarauniyar hanya.

Ma’aikatar baitil-malin Amurka ta bayyana shi a matsayin ɗan ta’adda na musamman a watan Satumban 2015, bisa dokar shugaban ƙasa (E.O) 13224, inda aka ƙaƙaba takunkumai na kuɗaɗe kan ƴan ta’adda da kuma waɗanda ke tallafa ma su ko ayyukan ta’addanci.

A watan Yunin 2014, ISIS, da kuma ake kira Da’esh, ta kwace ikon wasu yankuna na Syria da Iraƙi, tare da ayyana “Daular Musulunci,” da kuma ayyanaal-Baghdadi matsayin “Khalifa.” A shekarun baya,ISIS ta samu goyon baya daga ƙungiyoyi jihadi da masu tsattsauran ra’ayi daga sassan duniya, wanda ya haifar da hare-hare a duniya.

Wannan tukuicin yana da matuƙar muhimmanci a yaƙin da muke da ISIS. Kamar yadda aka samu galabar ISIS a fagen yaƙi, a shirye muke mu tabbatar tare da gano shugabannin ƙungiyoyin don ƙawancen ƙasashen duniya dake yaƙi domin kawar da ISIS za su ci gaba su tarwatsa ISIS da kuma daƙile duk wani burinta.

Karin Hotuna

Sami Jasim Muhammad al-Jaburi