Wanda ake nema
Bayani wanda zai kawo hukunci…

Salman Raoul Salman

Tukuicin Da Ya Kai Na Dala Milyan 7

Salman Raoul Salman yana tafiyad da goyon bayan ‘kungiyar yan ta’adda na Hizballah dake yammacin duniya. Jagora a ‘Kungiyar Tsaro na Waje na Hizballah (ESO), Salman yana da sa hannu a ‘kulle-‘kulle a duk fadin duniya. ‘Kungiyar ta ESO ‘bangare ne na Hizballah dake da alhakin shiryawa, daidaitawa, da kuma ‘kaddamar da hare-hare a wajen Lebanon. Suna kai hare-haren ne takamaimai akan Israliyawa da Amurkawa.

Daga cikin ‘kulle-‘kullen da Salman yake da sa hannu a ciki ya hada da tashin bom a cibiyar raya al’adu na ‘Kungiyar Juna ta Israliyawa da Argentinawa (AMIA). A ranar sha takwas ga watan Yuli, alif dubu daya da ‘dari tara da casa’in da hudu, Hizballah sun tashi mota mai ‘dauke da kayan fashewa a wajen cibiyar raya al’adu ta AMIA a Buenos Aires inda aka kashe mutane tamanin da biyar. Salman shi ne ya jagoranci kuma ya daidaita harin kai tsaye daga inda aka kai harin.

Sashin Taskar ‘kasar Amurka sun ‘nada Salman a ranar sha tara ga watan Yuli, shekara ta dubu biyu da sha tara a matsayin ‘dan ta’adda na musamman a duniya gaba ‘daya, bisa ga umarnin ‘bangaren mulkin ‘kasa 13224 saboda goyon bayan aiyukan ta’addancin Hizballah.

Karin Hotuna

Salman Raoul Salman
Salman Raouf Salman - English
Salman Raouf Salman - Arabic
Salman Raouf Salman - French
Salman Raouf Salman - Portuguese
Salman Raouf Salman - Spanish