Wanda ake nema
Bayani wanda zai kawo hukunci…

Salih al-Aruri

Tukuicin Da Ya Kai Na Dala Milyan 5

A cikin watan Oktoban shekara ta 2017, Salih Al-Aruri, daya daga cikin mutanen da suka kafa rundunar sojojin Izzedine al-Qassam, wani bangaren soji na kungiyar, an zabe shi a matsayin mataimakin shugaban Hukumar Siyasar Hamas. Al-Aruri yana samar da kudade da kuma aiwatar da ayukkan soji a Gabar Yammaci, an kuma alakanta shi da hare-haren ta’addanci da satar mutane da yin garkuwa da su. A cikin shekara ta 2014, al-Aruri ya sanar da hannun kungiyar Hamas a wani harin ta’addancin da aka kai a ranar 12 ga watan Yuni, shekara 2014 wanda aka sace da kashe wasu samarin Yahudawa a Gabar Yammaci, wanda ya hada da wani Bayahude mai shaidar zama dan kasa biyu, Isra’ila da Amurka, mai suna Naftali Fraenkel. Ya fito fili ya bayyana kisan a matsayin “aikin jarunta.” A cikin watan Satumba na shekara ta 2015, Sashen Baitulmalin kasar Amurka ya ayyana al-Aruri a matsayin Danta’addan Musamman na Kasa da Kasa (SDGT), biyo bayan Dokar Zartarwa wadda ta sa takunkumi kan duk kadarorin da ya mallaka, mai lamba 13224 .

Karin Hotuna

Lebanese Hizballah Poster - English
Lebanese Hizballah Poster - Arabic
Lebanese Hizballah Poster - Farsi
Lebanese Hizballah Poster - French