Wanda ake nema
Bayani wanda zai kawo hukunci…

Sajid Mir

Tukuicin Da Ya Kai Na Dala Milyan 5

Ana neman Sajid Mir ruwa a jallo, wani babban mamba na ƙungiyar ta’addanci ta ƙasashen waje da ke da zama a Pakistan Lashkar-e-Tayyiba (LeT) saboda hannu da yake da shi a hare-haren ta’addancin da aka kai a Mumbai na Indiya a watan Nuwamba na 2008. Shirin Ladan Adalci (Rewards for Justice program) ya yi alƙawarin bayar da tukuicin da ya kai dala miliyan 5 ga duk wanda ya ba da labarin da zai kai ga kamawa ko gurfanar da Sajid Mir a kotu a kowace ƙasa ce saboda rawar da ya taka a waɗannan hare-hare.

Tun daga ranar 26 ga Nuwamba, 2008, har zuwa Nuwamba 28, 2008, horarrun maharan LeT guda goma sun kai wasu jerin tsararrun hare-hare a gurare masu yawa a Mumbai, Indiya. Wuraren da aka kai wa harin sun haɗa da manyan otal-otal biyu (Taj Mahal Palace da The Oberoi), da Leopold Café, da gidan Nariman (Chabad), da tashar jirgin ƙasa ta Chhatrapati Shivaji. Sun kashe kimanin mutane 170. Amurkawa shida sun rasa rayukansu yayin harin. Amurkawan su ne: Ben Zion Chroman, Gavriel Holtzberg, Sandeep Jeswani, Alan Scherr, Naomi Scherr, da Aryeh Leibish Teitelbaum.

Sajid Mir ya kasance mai kula da ayyukan LeT a lokacin harin Mumbai. Ya taka rawa wajen tsarawa, shiryawa, da kuma aiwatar da harin. An gurfanar da Mir a Kotun Yanki ta Amurka, Gundumar Arewacin Illinois, sashin gabas ta (Chicago, Illinois) a ranar 21 ga Afrilu, 2011, kuma an tuhume shi da: haɗin baki don lalata da kadarorin gwamnatin wata ƙasar waje; ba da taimakon kayan aiki ga ‘yan ta’adda; taimakawa da kisan gilla ga wani ɗan ƙasa a wajen Amurka; da kuma jefa bama-bamai a wuraren amfani na jama’a. A cewar tuhumar, a yayin hare-haren Mir ya shawarci maharan da su kashe waɗanda suka yi garkuwa da su, da kunna wuta, da jefa gurneti. Bayan haka, ya nemi a yi musanyar wanda suka yi garkuwa da shi da wani mahari da aka kama. An bayar da sammacin kamo Mir a ranar 22 ga Afrilu, 2011. A cikin 2019, an saka Mir cikin Jerin sunayen ‘Yan Ta’addan FBI da ake nema ruwa a jallo.

A ranar 30 ga watan Agusta 2012, Ma’aikatar Baitul Malin ta sanya sunan Mir a ƙarƙashin Dokar Zartarwa ta 13224 sakamakon riƙe muƙamin jagoranci a cikin LeT. A cewar Ma’aikatar Baitulmalin Amurka, a shekarar 2005, Mir ya ba da horo ne ga masu aiki da ke shirin hayan ma’aikata zuwa ƙasashen waje da sace-sacen kuɗaɗe, da kuma gudanar da tsare-tsaren makirci. Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka ta ayyana LeT a matsayin ƙungiyar ta’addanci ta ƙasashen waje a cikin Disamba 2001.

Karin Hotuna

Sajid Mir