Aikin Ta’addanci
Bayani akan ...

Harin Bama-Bammai Akan Gidaje

Riyadh, Saudi Arabia| 13 ga Mayu, 2003

A ran 12 ga watan Mayun 2003 ne bama-bammai guda hudu suka tashi a gidaje ukku daban da juna dake a Roydh, Saudi Arabia. Wadanan gidajen mazaunu ne a wurin mutanen kasashen Yammacin Turai da yawa, tun ma ba Amurkawa da mutanen Ingila ba. Wannan harin ya hallaka jimillar mutane 20 da suka hada da Amurkawa 8, ya kuma raunana wasu mutane kusan 200. Al-Qaida ce ta shirya kuma ta aiwatarda wannan harin.

Shirin Bada Tukuici Don Adalci na tayin bada tukuicin da ya kai har na Dala milyan 5 ga duk wanda ya bada bayanin da zai kai ga kama wadanda suka kai wannan harin.