Labarin kan nasara

Ramzi Ahmed Yousef

Wanda aka yanke wa hukunci

Ramzi Yousef ne ummulhaba’isun shirya harin bam da aka kai kan Cibiyar Ciniki ta Duniya a watan Fabrairun 1993 a birnin New York, harin da ya hallaka mutane shidda, ya raunana fiyeda mutane dubu daya.Yousef da mukarabbansa sun tuka motar da aka shake da bama-bammai ne zuwa karkashin Cibiyar Ciniki. Sa’oi kalilan bayan kai harin, Yousef ya arce zuwa Pakistan ta cikin jirgin sama.

Daga baya ne Yousef ya bulla akasar Philippines inda ya shiga cikin wani sabon makirci na ta’addanci. Yousef ya shirya kashe Paparoma John Paul II ran 14 ga watan Janairun 1995 a lokacinda paparoman ke kan ziyarar aiki a nan Philippines sannan, kwannaki kalilan bayan haka, yaje ya tarwatsa jiragen saman Amurka guda 12 dake nahiyar Asia. Shirin baki dayansa an saka mishi lakabin “Oplan Bojinka” wanda lafazin Larabci ne da ma’anarsa itace “Shirin Fashe-Fashe-Fashe” ko “Shirin Karar Bindiga mai girma.” Koda yake Yousef ne babban jigon shirya wannan shirin na Oplan Bojinka, akwai wasu da suka taka rawa a cikin shirin kamar su Wali Khan Amin Shah, Abdul Hakim Murad, Khalid Shaikh Mohammad (kawun Yousef kuma babban jagaban shirya Harin 11 ga Watan Satumba) da kuma Hambali – dukkansu rikakkun ‘yan kungiyar al-Qaida.

Wani bangare na shirin da aka kulla shine cewa a rannakun 21 da 22 ga watan Janairun 1995, ‘yan ta’adda guda biyar zasu girka bama-bammai akan jiragen saman Amurka 12 da zasu yada zango a wasu kasashen Gabasci da Kudu-Maso-Gabashin nahiyar Asia a sashen farko na wannan tafiyar tasu; aka kuma shirya cewa ‘yan ta’addar zasu sauka kafin dukkan jirage su tarwatse yayinda suke sarari bisa tekun pacific. An umurci kowane daya daga cikin wadanan ‘yan ta’addar da ya shiga jirgi na biyu ko ma jirgi na ukku har sai sun kamalla shiga dukkan wadanan jiragen guda 12, su girka bama-bammai a cikin kowannensu. Jimillar mutanen da aka kiyasta zasu mutu a cikin wannan ta’addancin tafi mutane 4,000.

Sa’ar da aka yi shine cewa Yousef da mukarabban nashi sun yi sake, abinda ya janyo kasawar shirin da suka kulla. A ran 6 ga watan janairu, ala-tilas Yousef da Murad a guje suka fice daga gidansu dake Manila bayanda hayaki ya turnuke gidan a sanadin kamawa da wuta da wani gamin a kayan guba yayi, har hayakin ya rinka fita ta cikin taga. Yousef ya nemi Murad da ya koma cikin gidan, ya dauko wata kwamputa da sauran tarkaccen kayan da zasu iya zama sheda mai muni a wurinsu. Sai dai kuma yayinda Murad ya koma gidan, ya yi kicibis da ‘yansanda wadanda ashe har sun riga sun iso wurin. Shi kuma Yousef, da ya ga an cafke Murad, sai ya arce zuwa Pakistan.

A cikin watan fabrairu na 1995 ne wani mai bada bayani da yaga sakkonnin RFJ na bada goron tukuci, ya garzaya zuwa Opishin Jakadancin Amurka dake Islamabad inda ya bada labarin da ya taimaka aka gano inda Yousef yake. A ran 7 ga watan Fabrairun 1995 hukumomin Pakistan, tareda taimakon ma’aikatan tsaro na musamman na M a’aikatar harakokin Wajen Amurka, suka cafke Yousef a Islamabad, Pakistan, kuma suka maido shi zuwa Amurka. Yanzu haka Yousef yana wani gidan kurkuku dake jihar Colarado. Su ma sauran mutane hudu dake da hannu wajen shata shirin Oplan Bojinka, an kama su.