Wanda ake nema
Bayani wanda zai kawo hukunci…

Ramadan Abdullah Mohammad Shallah

Tukuicin Da Ya Kai Na Dala Milyan 5

Ana neman Ramadan Abdullah Mohammad Shallah a bisa zargin kitsa makircin gudanarda aiyukkan Kungiyar Jihadin Islamiyya ta Palesdinu (PIJ), wacce kungiyar ta’addanci ce, ta hanyar anfani da matakan sayarda kayan haramun da saka bama-bammai, kisa, kwace da kuma juyarda kudade ta hanyar da doka bata yard aba.

Shallah yana cikin mutanen farko da suka kafa kungiyar PIJ kuma tun 1995 yake rike da mukamin Babban Sakatare kuma shugaban kungiyar wacce helkwatarta ke a birnin Damascus na kasar Syria.

An kira Shallah “Dan ta’adda Na Musamman” a karkashin Dokar Amurka a ran 27 ga watan Nuwamban 1995, kuma a shekarar 2003 a Kotun Tarayya ta Gundumar Florida ta Tsakiya, an zarge shi da aikata laifukka 53.

Karin Hotuna

Ramadan Abdullah Mohammad Shallah