Wanda ake nema
Bayani wanda zai kawo hukunci…

Radullan Sahiron

Tukuicin Da Ya Kai Na Dala Milyan 1

Radullan Sahiron babban kusaa ne a kungiyar Abu Sayyaf (ASG) dake a Philippines. Wannan kungiyar ta tuzgo ne daga cikin babbar kungiyar Fafatikar Neman ‘Yancin Mutanen Moro a farkon shekarun 1990s a karkashin jagorancin Abdurajak Abubakar Janjalani wanda aka kashe a gumurzun da aka yi da ‘yan sandan Philippines a shekarar 1998. Kanensa Khadaffy Janjalani ne ya gaje shi a matsayin shugaban kungiyar. Shima Khadaffy Janjalani an kashe shi a wani fadan da aka yi da sojan Philippines a watan Satumbar 2006. Yanzu ana sa ran cewa Radullan Sahiron shine sabon shugban kungiyar ta ASG.

Mutane masu yawa da ba ruwansu da komai da suka hada maza, mata da yara sun rasa rayukansu ko sun sami munanan raunukka a sanadin halayen Sahiron. Sahiron ya taka muhimmiyar rawa a cikin sacewar da aka yi wa wasu Amurkawa guda ukku da suka hada da Martin da Gracia Burnham da wasu ‘yan Filifino su 17 daga wurin shakatawar maziyartan Palwa dake Philippines a cikin watan Mayun 2001. An kuma kashe da yawa dsaga cikin wadanda aka yi garkuwa da su, ciki harda Ba’Amurke, Guillermo Sobero.

Ana jin har yanzu Sahiron na ci gaba da zama a boye a kudancin Mindanao inda yake ci gaba da kitsa makircin aiyukkan ta’addancin dake shahuwar dimbin al’umma. Saboda matsayinshi a cikin kungiyar ASG wacce ta’addancinta ya yi sanadin mutuwar ‘yan Amurka da Phiippines masu yawa, Amurka na wa Sahiron daukan cewa shi barazana ne ga rayukkan mutanen Amurka da Philippines da kuma kadarorinsu.

Sahiron ya rasa hannunsa na dama a cikin yaki da ma’aikatan tsaro a farkon shekarun 1970s. Ya iya magana da harsunan Larabci da na Tausug.