Labarin kan nasara

Qusay Hussein

Marigayi

Qusay Hussein shine karami a cikin ‘ya’yan Saddam guda biyu maza da ya haifa daga aurensa na afarko kuma an sa ran cewa shine wanda zai dauki ragamar mulki bayan mutuwar mahaifinsu, Saddam. Qusay ne ya kasance shugaban Hukumar ‘Yansandan Asiri ta Iraq, Hukumar Aiyukkan Tsaro, Rundunar Soja ta republican da kuma Rundunar Musamman ta Sojan Republican wacce aka dauka a duk kasar cewa itace rundunar soja mafi karfi a tsakanin sojojin Iraq.

Bayanin da wani sheda ya bada a ran 23 ga watan Yulin 2003 ne ya kai ga a gano inda Uday da Qusay Hussein suke. Tareda taimakon Bataliyar mayakan Sama ta 101 ne rundunar soja ta 20 ta kai samamen kama wadanan mutanen. An gwabza yaki na sa’oi hudu wanda ya zama sanadin a kashe Uday da Qusay Hussein.