Wanda ake nema
Bayani wanda zai kawo hukunci…

Qasim al-Rimi

Tukuicin Da Ya Kai Na Dala Milyan 10

An nada Qasim al-Rimi Emiyan AQAP, cikin watan Yuni na shekarar 2015, nan take bayan yayi rantsuwar hadin gwiwa da shugaban kungiyar al-Qa’ida Ayman al-Zawahiri kuma yayi kira da a sabunta kai hare-hare ga kasar Amurka. Al-Rimi ya horar da ‘yanta’adda a sansanin kungiyar al-Qa’ida dake kasar Afghanistan a cikin shekarun 1990, kuma daga baya ya koma kasar Yemen inda ya zama kwamandan sojan kungiyar AQAP. An yanke mashi hukuncin zama gidan yari na tsawon shekaru biyar a kasar Yemen cikin shekara ta 2005, kan laifin kitsa kashe Jakadan kasar Amurka, kuma ya gudu a cikin shekara ta 2006. An alakanta Al-Rimi da harin da aka kai ma ofishin Jakadancin Amurka dake Sana’a a cikin shekara ta 2008, wanda yayi sanadiyyar mutuwar wasu masu gadi ‘yan kasar Yemen su 10, da farar hula hudu, da wasu ‘yan ta’adda shidda. An kuma alakanta Al-Rimi da wani harin kunar bakin wake na “dan kamfai” da Umar Farouq Abdulmutallab ya so kaddamarwa a cikin wani jirgin saman kasar Amurka a cikin watan Disamba na shekarar 2009. Acikin shekara ta 2009, gwamnatin kasar Yemen ta zarge shi da gudanar da wani sansanin horarwar kungiyar al-Qa’ida a gundumar Abyan na kasar Yemen.

A cikin wani faifan bidiyon ranar 7 ga watan Mayu na shekara ta 2017, yayi kira ga magoya bayansa dake zaune a kasashen Yammacin duniya da su kaddamar da “saukakakkin” hare-hare da yabo ga Omar Mateen, wanda ya kashe mutane 49 a cikin wasu harbe-harben game-gari cikin watan Yuni na shekarar 2016 da aka yi a mahadar-dare dake garin Orlando Florida.

A cikin watan Mayu na shekarar 2010, Sashen Harkokin waje ya ayyana al-Rimi a matsayin Danta’addar Kasa-da-kasa da Namusamman, a karkashin Dokar Zartarwa mai lamba 13224. A cikin watan Mayu na shekara 2010, an sa al-Rimi cikin jerin sunayen mutanen dake da alaka da kungiyar ISIL ta al-Qa’ida wanda Kwamitin sanya Takun-kumi na Majalisar dunkin duniya ke tsarawa. An bada sanarwar ladar dalar Amurka miliyan 5 ga wanda ya bada rahoto kan al-Rimi, a ranar 14 ga watan Oktoba na shekarar 2014.

Karin Hotuna

Qasim al-Rimi
al-Rimi and Batarfi English PDF
al-Rimi and Batarfi Arabic PDF
AQAP English PDF
AQAP Arabic PDF