Aikin Ta’addanci
Bayani akan ...

Satar Jirgin Saman Pan Am mai lamba 73v

Karachi, Pakistan | 5 ga Satumba, 1986

Ma’aikatar Harakokin Waje ta amince da a bada tukuicin Dala milyan 5 ga duk wanda ya bada bayanin da ytasa aka kama ko gurfanarda kowanne daga cikin wadanan mutanen: Wadoud Muhammad Hafiz al-Turki, Jamal Saeed Abdul Rahim, Muhammad Abdullah Khalil Hussain al-Rahayyal da Muhammad Ahmed al-Munawar – wadanda dukansu ake daukar ‘yan kungiyar ta’addanci ta Abu Nidal ne.

A lokacinda yake ajiye a Karachi, Pakistan ne, da midsalin karfe 6 na safiyar ranar 5 ga watan Satumbar 1986 ‘yan kungiyar Abu Nidal suka sace jirgin saman kampanin Pan Am mai lamba 73. A lokacinda aka sace jirgin, matafiya 379 da ma’aikatan jirgin, ciki harda Amurkawa 78, duk suna cikin jirgin. Ma’aikatan jirgin sun gudu, suka bar jirgin yadda ba’a iya tuka shi. Barayin jirgin sun kame shi sosai sannan suka nemi ma’aikatan jirgin da cewa su zo a tafi da jirgin da wadanda ke cikinsa zuwa Cyprus. A lokacinda ake sace jirgin, an kashe Ba’murke daya a bakin kofar jirgin. A karshen satar jirgin ne kuma barayin jirgin suka bude wuta akan pasinjojin dake ciki. Akalla matafiya 20 aka kashe, wasu fiyeda 100 suka sami raunukka.

A nan inda abin ya faru hukumomin Pakistan suka kame hudu daga cikin wadanda ake zargi da satar jirgin, sannan suka kama mutum na biyar da akace ya taimaka wajen kai harin. Dukkan mutanen biyar, ciki harda hudun da aka ce za’a bada tukuici a kansu, an kama su, anyi musu shara’a kuma an yanke musu hukucin zaman gidan kurkuku.

A cikin watan Satumbar 2001 ne Hukumomin Pakistan suka saki Zayd Hassan Abd-al-Latif Safarini, daya daga cikin ‘yan ta’addar da aka yankewa hukunci. DSaga baya Hukumar FBI ta sake kama shi kuma aka yi mishi shara’a a watan Kotun Tarayya ta Amurka. A ran 16 ga watan Disambar 2003 ne Safarini ya yarda da wata yarjejeniya gameda karar da Ma’aikatar Shara’a ta Amurka ta tsara. Ran 13 ga watan Mayun 2003 ne aka yanke mishi hukuncin daurin shekaru 160 a kurkuku.

A cikin wsatan Janairun 2008 ne Hukumomin Pakistan suka saki mutane hudun nan da ake tayin bada tukuici a kansu. Daman a Kotun Gundumar Columbia ne aka zaergi Wadoud Muhammad Hafiz al-Turki, Jamal Saeed Abdul Rahim, Muhammad Abdullah Khalil Hussain ar-Rahayyal da Muhammad Ahmed al-Munawar da laifin taka rawa a cikin satar jirgin, kuma har yanzu suna sake, ba’a kama su ba.

Don neman kariun bayani, dubi “Wadanda Ake Nema Don Ta’addanci”

Wadoud Muhammad Hafiz al-Turki

Muhammad Ahmed al-Munawar

Muhammad Abdullah Khalil Hussain ar-Rahayyal

Jamal Saeed Abdul Rahim