Aikin Ta’addanci
Bayani akan ...

Harin Bam akan Jirgin Saman Pan Am mai lamba 103

Lockerbie, Scotland | 21 ga Disamba, 1988

A ranar 21 ga watan Disambar 1988 ne aka yi wa jirgin saman kampanin Amurka na Pan Am mai lamba 103, kirar Boeing 747 da ya tyaso daga filin jirgin saman Heathrow na London ta Ingila dake kan hanyarsa zuwa filin jirgin saman JFK dake New York yayi kaca-kaca lokacinda wata nakiyar da aka boye a cikin kaya ta fashe a cikin sashen ajiye kaya na jirgin. Wannan fashewar ta janyo mutuwar dukkan matafiya 259 dake cikin jirgin, cikinsu harda Amurkawa 189 da kuma mazaunan garin Lockerbie na kasar Scotland su 11.

A ran 13 ga watan Nuwamban 1991 ne Kotun Tarayya ta Gundumar Columbia ta tuhumci wakilan gwamnatin Libya Abdel Basset Ali Mohamed al-Megrahi da kuma Al Amin Khalfia Fhimah “tareda wasu da Mahukata basu sani ba” da laifin Kitsa Makircin lalata Jiragen saman Amurka, Kashe Amurkawa da kuma sauran tuhumce-tuhumce na mallakar abubuwa masu favshew. Kashegari ne lauyan Lord ya bada sanarwar cewa an kuma tuhumci al-Megrahi da Fhimah da laifukkan kulla makirci da kisan gilla a kasar Scotland.

A ran 31 ga watan janairun 2001 ne wani rukunin alkallai ukku suka sami al-Megrahi da laifin kashe dukkan mutane 270 dake cikin wannanj jirgin na Pan Am mai lamba 103 a cikin sararin samaniya da kuma wadanda suka rasa rayukkansu a kasa a Lockerbie. An yanke mishi hukuncin da aka tanada da daurin rai da rai da kuma tanadin cewa dole ne sai ya share akalla shekaru 27 a gidan kurkuku kafin ya iya neman alfarmar a yi mishi ahuwar saki. Shima abokin aikata laifin nasa, Fhimah an same shi da laifi kuma an aika shi ta jirgin sama zuwa Tripoli, Libya. A ran 14 ga watan Maris na 2004 ne wani kwamitin alkallai biyar na babbar Kotun Scotland ta tabattarda wannan hukuncin wanda yassa aka dauke shi zuwa vcan Scotland don ya fara zaman kurkuku na hukuncin da aka yanke masa.

Bayan bukatar da aka nema daga Hukumar Nazarin Sahara’oi ta kasar Scotland (SCCRC) a cikin watan Yunin 2007 ne, aka yardarm wa al-Megrahi damar ya nemi daukaka karar shi.Yayinda ake jiran jin amsar wannan bukatar ne a watan Satumbar 2008, aka gano cewa al-Megrahi ya kamu da cutar sankara mai kisa. A ran 20 ga watan Agustar 2009, a bisa shawarar Hukumar lafiya ta Gidajen Yarin Scotland na cewa duk-duk kasa ga wattani ukku suka rage wa al-Megrahi a raye, kuma bayan shi al-Megrahi ya jane wasikar bukatar da ya nema ta daukaka shara’arsa ne, Sakataren majalisar ministocin Scotland ya amince da wasikar neman a sake shi a bisa hujjar jinkayi da l-Megrahi ya shigar. Idan aka hada zaman kurkuku da yayi kafin a yanke mishi hukunci, za’a ga cewa duka-duka al-Megrahi ya share shekaru fiyeda 10 na hukuncin da aka yanke mishi, kafin a sake shi. A wannan ranar ta yau, ana sa ran cewa har yanzu al-megrahi da Fhimah dsuna ci gaba da zama a birnin Tripoli.

Saboda imanin da tayi na ba al-Megrahi da Fhimah kadai ne ke da alhakin saka bam din da ya tarwatsa jirgin saman Pan Am mai lamba 103 ba, yassa Ma’aikatar harakokin wajen Amurka ta yarda a yi tayin bada goron tukuicin Dala milyan 5 ga duk wanda ya bada bayanin da zai kai ga kama sauran mutanen dake da alhakin saka wannan bam akan jirgin saman na Pan Am 103 da kuma kashe matafiya 270 dake cikinsa.