Wanda ake nema
Bayani wanda zai kawo hukunci…

Mu‘taz Numan ‘Abd Nayif Najm al-Jaburi

Tukuicin Da Ya Kai Na Dala Milyan 5

Mu’taz Numan ‘Abd Nayif Najm al-Jaburi, wanda kuma ake kira Hajji Taysir babban jigo ne a ƙungiyar Daular Musulunci (ISIS) a Iraƙi da Syria kuma babban mamba a ƙungiyar al-Ƙa’ida (AQI) da ta gabace ta.

Al-Jaburi ya jagoranci samar da bama-bamai ga ta’addancin ISIS da ayyukanta na ta’addanci.

A watan Yunin 2014, ISIS, da kuma ake kira Da’esh, ta kwace ikon wasu yankuna na Syria da Iraki, tare da ayyana “Daular Musulunci,” da kuma ayyanaal-Baghdadi matsayin “Khalifa.” A shekarun baya,ISIS ta samu goyon baya daga kungiyoyi jihadi da masu tsattsauran ra’ayi daga sassan duniya, wanda ya haifar da hare-hare a duniya.

Wannan tukuicin yana da matukar muhimmanci a yakin da muke da ISIS. Kamar yadda aka samu galabar ISIS a fagen yaki, a shirye muke mu tabbatar tare da gano shugabannin kungiyoyin don kawancen kasashen duniya dake yaki domin kawar da ISIS za su ci gaba su tarwatsa ISIS da kuma dakile duk wani burinta.

Karin Hotuna

Mu‘taz Numan ‘Abd Nayif Najm al-Jaburi