Wanda ake nema
Bayani wanda zai kawo hukunci…

Musa Asoglu

Tukuicin Da Ya Kai Na Dala Milyan 3

Musa Asoglu babban jigo ne a cikin kungiyar Juyin Juya Hali ta Turkiya (wacce a harshen Turkanci ake kira: Devrimci Halk Kurtuluş Partisi Cephesi ko DHKP/C). Kungiyar DHKP/C ta jima tana auna kadarorin Amurka har ma da sojoji, ma’aikatu da ma’aikatan soja da na diplomasiyar Amurka tun daga lokacinda aka kafa ta a 1994, lokacinda kungiyar da ta gada ta Devrimci ko Dev Sol ta wargaje zuwa kungiyoyi daban-daban. Manufarta dai itace ta goge duk wanta alama ta Amurka da NATO daga Turkiya, ta maye gurbinsu da kasa mai bin tafarkin kwaminisanci. A cikin watan Fabrairun 2013 ne wani dan kunar bakin wake da da alaka da kungiyar ya kai hari akan Opishin Jakadancin Amurka dake Ankara, har ya kashe wani dogari dan Turkiya.Tun shekarar 1997 Ma’aikatar Harakokin Wajen Amurka ta kaddamarda kungiyar DHKP/C a matsayin kungiyar ta’addanci, sannan ta sake nazarin wannan kuma ta sake sabunta shi a ran 24 ga watan Yulin 2013.

A cikin shekarun 1990s Musa Asoglu ya shiga kungiyar DHKP/C, lokacin yana zaune a kasar Holland. An bada rahoton cewa ya dauki akalar jagorancin kungiyar ne bayanda wanda ya kafa ta, Dursun Karatas, ya mutu a shekarar 2008. Asoglu wakili ne a cikin majalisar kungiyar DHKP/C, kwamitin da shine wuka da namar yanke hukunci a kungiyar, kuma ana jin shine ma shugaban kwamitin tara kudade da sarrafa kudaden kungiyar a kasashen Turai. Ance ma shine ya bada umurnin a kai harin kunar bakin waken nan da aka kai kan Opishin Jakadancin Amurka dake Ankara a ran 1 ga watan Fabrairun 2013, inda har aka akshe wani dogari, dan Turkiya. Ance kuma shine ke da hakkin harin da aka kai a watan maris na 2013 akan helkwatar Jam’iyyar AKP da kuma Ma’aikatar Shara’a ta Turkiya.

Musa Asoglu, Zerrin Sari da Seher Demir duk manyan shugabanni ne na kungiyar Juyin Juya Hali ta Turkiya ta DHKP/C (wacce a harshen Turkanci ake kira:: Devrimci Halk Kurtuluş Partisi Cephesi, or DHKP/C).

Karin Hotuna

Karin Hoton Musa Asoglu
Karin Hoton Musa Asoglu
Karin Hoton Musa Asoglu