Wanda ake nema
Bayani wanda zai kawo hukunci…

Murat Karayilan

Tukuicin Da Ya Kai Na Dala Milyan 5

Murat Karayilan, shugaban Rundunar Bada Kariya ga Mutane (HPG) kuma babban shugaban kungiyar PKK. Yana yin aiki a Sashen Baitulmali. Gwamnatin kasar Turkiyya ta sa masa laifin haddasa hare-haren ta’addanci.

Jam’iyyar Ma’aikata ta Kurdistan (PKK), wadda kuma aka sani da suna Kongra-Gel kungiyar ta’addancin yanki ce wadda kasar Amurka ta bayyana a matsayin Kungiyar Ta’addanci ta Kasa-da-kasa (FTO). Kungiyar PKK ta kai hare-hare ga ma’aikatan gwamnati, ‘yansanda da jami’an tsaro, kuma ta sha jikkata da kashe fararen hula. Kungiyar PKK na amfani da abokan huldarta da ayukkan ta’addanci a fadin nahiyar Turai don samun makamai da kayan aiki. Kungiyar PKK tayi amfani da ‘yan kunar bakin wake, da abubuwan dake tarwatsewa da ake sawa a jikin abun hawa (VBIEDs), da sauran dabarun ta’addanci. Kungiyar PKK kuma tana dauka da koyar da matasa aikin ta’addanci, a wasu lokutta ta hanyar sace su da daukar su aikin soji. A cikin shekarar 1993, kungiyar PKK ta sace masu yawon bude ido 19 da suka fito daga kasashen yammacin duniya wadanda suka hada da wani Ba’amurke, kuma cikin shekarar 1995 wasu Amurkawa biyu sun jikkata a cikin wani harin bom na kungiyar PKK.

A cikin shekarar 2015 da 2016, kungiyar PKK ta fadada hare-haren da take kaiwa a cikin kasar Turkiyya, da cibiyoyin yankuna, da wuraren bude ido dake bakin Mediteranea da Aegean na kasar Turkiya. A cikin watan Ogusta 2016, kungiyar tayi ikirarin alhakin kai wani harin bom din da aka kai da mota kan hedikwatar ‘yansanda ta Sirnak, inda aka kashe mutane 11 kuma aka jikkata sama da mutane 70. A cikin watan Yuni 2017, kungiyar PKK ta kai hari kan wani jerin gwanon sojoji a kudu maso gabashin kasar Turkiyya, wanda ya kashe sama da sojoji 20. Tun shekara ta 2015, kungiyar nada alhakin mutuwar farar hula da jami’an tsaro sama da 1,200.

Karin Hotuna

PKK Poster - English
PKK - Kurdish Poster
PKK - Turkish Poster