Aikin Ta’addanci
Bayani akan ...

Harare-Haren Mumbai na Shekarar 2008

Mumbai, Indiya | Nuwamba 26-29, 2008

Farawa da ranar 26 ga watan Nuwamba, 2008, cigaba har zuwa ranar 29 ga watan Nuwamba, 2008, masu kai hari su goma da suka samu horo daga wata kungiyar ta’addanci ta kasar waje dake zaune a kasar Pakistan mai suna Lashkar -e- Tayyiba (LeT) suka kai jerin wasu hare-haren da aka shirya kan wasu wurare a Mumbai, Indiya, wadanda suka hada da Taj Mahal otel, da Oberoi otel, da wurin sayar da kayan makulashe na Leopold, da Gidan Nariman (Chabad) da kuma tashar jirgin kasa ta Chahatarapati Shivaji, inda aka kashe akalla mutane 170.

An kashe Amurkawa shidda a cikin hare-haren na kwana ukku, wadanda suka hada da: Ben Zion Chroman, da Gavriel Holtzberg, da Sandeep Jeswani, da Alan Scherr, da diyar shi mai suna Naomi Scherr, da kuma Aryeh Leibish Teitelbaum.

Shirin Bada La’ada don Adalci na tayin bada la’adar dalar Amurka Miliyan 5 ga duk wanda ya bada wani bayani game da mutanen dake da hannu cikin kai wadannan hare-haren. Mutanen dake kan gaba wurin kitsa munanan hare-haren sun gudu, kuma wannan binciken da ake yi na nan daram yana gudana. Za a bada wannan la’adar ne ga duk wani bayani kan duk wani mai hannu a cikin wannan aikin ta’addanci.

Wata kotun tarayya a kasar Amurka ta zargi David Ceman Headley da Tawwur Rana a taimaka ma ayukkan hare-haren kungiyar LeT. A cikin watan Janairun 2013, Headly, wani Ba’amurke mai ruwan asalin kasar Pakistan, an yanke masa hukuncin daurin shekaru 35 a gidan yari kan samun shi da laifukan ta’addancin tarayya har goma sha-biyu, masu alaka da rawar da ya taka ta kitsa hare-haren ta’addancin Nuwamba 2008 da aka kai a Mumbai, Indiya, da wani harin baya da aka shirya kaiwa ga wani kamfanin jaridar dake kasar Denmark. Acikin watan Maris 2010, ya karbi laifinsa na aikata dukkan laifukka 12 da ake zargin shi da aikatawa, wadanda suka hada da taimakawa da karfafawa wurin kisan da aka yi ma Amurkawa shidda. Kotu ta yanke ma Headley hukunci kan hada baki don tada bom a wuraren al’umma a kasar Indiya; hada baki don kashewa da jikkata mutane a kasar Indiya; da caji kan laifuka shidda na taimakawa da karfafawa wurin kisan Amurkawa shidda a kasar Indiya; da hada baki don samar da kayan aikata ta’addanci a kasar Indiya; da hada baki don kashewa da jikkata mutane a kasar Denmark; da hada baki don samar da kayan aikata ta’addanci a kasar Denmark, da kuma hadabaki don samar da kayan aikata ta’addanci ga kungiyar LeT. Rana, wani dan kasar Kanada, kuma tsohon abokin Headley, kotu ta yanke ma shi hukuncin daurin shekaru 14 kan laifin hada baki don samar da kayan aikata ta’addanci wurin shirya kai harin ta’addancin da aka yi a kasar Denmark, da kuma samar da taimakon kayan aikata ta’addanci ga kungiyar LeT. A cikin watan Yuni 2011, kotu ta wanke Rana daga aikata laifin hada baki don samar da kayan aikata ta’addanci a harin ta’addancin da aka kaddamar cikin watan Nuwamba 2008 a Mumbai, amma an yanke ma shi hukunci kan hannu a hadin bakin shirya kai harin ta’addanci ga wani kamfanin jaridar kasar Denmark, da kuma bada tallafin kayan aikata ta’addanci ga kungiyar LeT.

Suma wadannan mutanen da ake tuhuma wata kotun tarayya ta kasar Amurka na zargin su da hannu a cikin ta’addanci:

  • Sajid Mir – wanda ya kasance “mai horarwa” ga David Headley da sauran wadanda aka ba umurnin su gudanar da ayukkan da suka danganci kitsawa, shiryawa da kaddamar da hare-haren ta’addanci a madadin kungiyar LeT
  • Major Iqbal – wani mazaunin kasar Pakistan wanda ke da hannu a tsarawa da samar da kudaden kaddamar da hare-haren da kungiyar LeT tayi.
  • Abu Qahafa – wani mazaunin kasar Pakistan dake da alaka da kungiyar LeT, wanda ya koyar da wasu dabarun yakin da ake amfani da su wurin kai harin ta’addanci
  • Mazhar Iqbal, wanda aka fi sani da suna Abu al – Qama – wani mazaunin kasar Pakistan kuma daya daga cikin kwamandodin Let

Karin Hotuna

Mumbai Attacks - English PDF
Mumbai Attacks - Baluchi PDF
Mumbai Attacks - Hindi PDF
Mumbai Attacks - Pashto PDF
Mumbai Attacks - Urdu PDF