Wanda ake nema
Bayani wanda zai kawo hukunci…

Muhammad Khadir Musa Ramadan

Tukuicin Da Ya Kai Na Dala Milyan 3

Muhammad Khadir Musa Ramadan, babban kusa ne kuma fitaccen mai yada manufa na kungiyar Islamic State ta Iraki da Siriya (ISIS). An haifi Ramadan, wanda kuma aka sani da Abu Bakr al-Gharib, a kasar Jordan.

Ramadan daya ne daga jami’an yada labarai na ISIS da suka fi dadewa wanda kuma ya ke kula da ayyukan kafafen watsa labaran kungiyar na yau da kullum, da suka hada da sarrafa bayanai daga gungun magoya bayan ISIS da ke warwatse a fadin duniya. Ramadan ya taka gagarumar rawa a ayyukan farfagandar ISIS na ta’addanci domin cusa tsattsauran ra’ayi, dauka, tare da tunzura mutane a fadin duniya. Ya jagoranci shiryawa, tsarawa tare da samar da faya-fayen bidiyo, takardun bayanai, da kuma shafukan kan intanet masu yawa da suka kunshi hotunan azabtarwa da kisan kiyashi na fararen hula wadanda ba su yi laifin komai ba. Karin tabbatarwa kan tsattsauran ra’ayinsa na ta’addanci, ya jagoranci wani yunkuri na kakkabe masu saukin ra’ayi daga ISIS, inda ya daure membobin reshen farfaganda na ISIS wadanda ba su da tsattsaurar fahimtar Musulunci irin ta sa.

Karin Hotuna

Muhammad Khadir Musa Ramadan
Muhammad Khadir Musa Ramadan