Wanda ake nema
Bayani wanda zai kawo hukunci…

Muhammad Ahmed al-Munawar

Tukuicin Da Ya Kai Na Dala Milyan 5

Ana neman Muhammad Ahmed al-Munawar ne dangane da rawarsa a cikin sace jirgin saman kampanin Pan Am mai lamba 73 a ran 5 ga watan Satumbar 1986 yayinda jirgin ke zaune a kasa a Karachi, Pakistan. Ana zargin wannan mutumen dake sama da aikata wadanan laifukkan:

Kitsa makircin aikata laifukka akan Amurka; makircin kashe Amurkawa a wajen Amurka; kashen Amurkawa a wajen Amurka; yunkurin kashe Amurkawa a wajen Amurka; yiwa Amurkawa mummunan raunukka a wajen Amurka; sace mutane; anfani da makami wajen aikata laifin tashin hankali; girka wani abu mai lahani a cikin jirgin sama; yi wa wani mutum dake cikin jirgi lahani ga jikinsa; satar jirgin sama a sararin samaniya; lalata jirgin sama da gangan da kuma taimakawa da bada tallafi wajen aikata laifi.

An Zargi Muhammad Hafiz al-Turki, Jamal Saeed Abdu Rahim, Muhammad Abdullah Khalil Hussain ar-Rahayyal da Muhammad Ahmed al-Munawar a Gundumar Columbia da laifin taka frawa a sace jirgin saman kampanin Pan Am mai lamba 73 a ran 5 ga wqatan Satumbar 1986 yayinda jirgin ke zaune kasa a Karachi, Pakistan. Bayan sun rike jirgin da mutane 379 dake cikinsa da suka hada da Amurkawa 78 har na tsawon sa’oi 16 ne, wadanda suka sace jirgin suka shiga bude wuta akan pasinjojin, inda karshenta suka kashe akalla mutane 20, suka raunana wasu sunfi 100. Ana sa ran cewa wadanda suka cinna wannan ta’asar ‘yan kungiyar Abu Nidal ce, wata kungiyar ta’addanci ta kasa-da-kasa.

Karin Hotuna

Hoton Muhammad Ahmed al-Munawar