Wanda ake nema
Bayani wanda zai kawo hukunci…

Muhammad al-Jawlani

Tukuicin Da Ya Kai Na Dala Milyan 10

Muhammad al-Jawlani, wanda kuma aka sani da Muhammad al-Golani, wanda kuma aka sani da Muhammad al-Julani, babban jagora ne na ƙungiyar ta’addanci, wato al-Nusrah Front (ANF), reshen Syria na al-Qa’ida.

A watan Aprilu, al-Jawlani ya yi mubaya’a ga al-Qa’ida da kuma jagoranta Ayman al-Zawahiri. A watan Yuli 2016, al-Jawlani ya yabawa al-Qa’ida da al-Zawahiri a wani faifan bidiyo na yanar gizo kuma ya yi iƙirari cewa ANF zata canza sunanta zuwa Jabhat Fath Al Sham (“Kame Filayen Daga”).

A ƙarƙashin jagorancin al-Jawlani, ANF ta ƙaddamar da jerin hare-haren ta’addanci a Syria, wasu lokuta da suke harar fararen hula. A watan Aprilu na 2015, an bayar da rahoton cewa ANF ta sace mutane, kuma daga bisani ta saki a ƙalla fararan hula Ƙurdawa 300 daga wani wurin duba abuben hawa a Syria. A watan Yuni 2015, ANF ta ɗauki alhakin hallaka mutane 20 mazauna ƙauyen Druze na Qalb Lawzeh a gundumar Idlib, Syria.

A watan Janairu 2017, ANF ta haɗe tare da wasu ƙungiyoyin adawa masu tsaurin ra’ayi domin kafa Hayat Tahrir al-Sham (HTS). ANF ta ci gaba da zama ɓangaren al-Qa’ida a Syria. Yayinda al-Jawlani ba shine jagoran HTS ba, ya ci gaba da zama jagoran ANF, wacce take jigon HTS.

An tabbatar da ANF a matsayin Ƙungiyar Ta’addanci a Ƙasashen Waje (FTO) a ƙarƙashin Dokar Shige-da-fice da Zamantowa ɗan Ƙasa da kuma Tabbatarwa ta Musamman a kan Ƙungiyoyin Ta’addanci a Duniya ƙarƙashin E.O 13224. Kwamitin Saka Takunkumi na Kwamitin Tsaro na Majalisar Ɗinkin Duniya a kan ISIL (Da’esh) da al-Qa’ida ya daɗa ANF a jerinsa na saka tukunkumi.

Sashin Tsaro na Ƙasa ya tabbatar da Al-Jawlani a matsayi na Musamman na Ɗan Ta’adda a duniya (SDGT) a ƙarƙashin Doka ta 13224 ta Gwamnati. Kuma an saka shi a jerin Takunkumi na Kwamitin Tsaro na Majalisar Ɗinkin Duniya a kan ISIL (Da’esh) da al-Qa’ida.

Karin Hotuna

Muhammad al-Jawlani English Poster
Muhammad al-Jawlani