Wanda ake nema
Bayani wanda zai kawo hukunci…

Mohamed Makawi Ibrahim Mohamed

Tukuicin Da Ya Kai Na Dala Milyan 5

A ran 1 ga watan Janairun 2008 ne aka harbe kuma aka kashe Ba’Murke kuma ma’aikacin Hukumar Raya Kasa ta Amurka (USAID) John Granville da direbansa dan kasar Sudan, Abdelrahman Abbas rahama a lokacinda suke kan hanyarsu ta komawa gida bayan bikin Jajibirin Sabuwar Shekara da suka halarta a Khartoum, Sudan. A rarrabe, kungiyoyi biyu suka dauki alhakin kai wannan harin: Ansar al-Tawhid (Magoya bayan Akidar Kadaicin Allah Guda) da kuma al-Qaida a Kasar Tapkunan Nilu Biyu (AQTN).

Hukumomin shara’ar Sudan sunyi wa mutane biyar shara’a kuma sun yanke musu hukunci akan rawar da suka taka cikin wadanan kashe-kashen. An yanke hukuncin kisa ta hanyar ratayewa akan Abu Zaid Mohamed Hamza, Mohamed Makawi Ibrahim Mohamed, Abdelbasit Alhaj Alhassan Haj Abdelraouf Hamad, da kuma Mohanad Osman Yousif Mohamed, sai dai kuma sun gudu shekara daya bayan yanke musu hukuncin. Mohanad ya rasu ne a Somalia cikin watan mayun 2011, shi kuma Abdeltaouf hukumomi sun sake cafke shi daga baya. Har yanzu ba’a kama Makawi da Abdelbasit ba.

Makawi yana da alaka da wata kungiya dake Sudan da ake kira al-Qaida a Kasar Tapkunan Nilu Biyu wacce ke kulla makarkashiyar kai hare-hare akan kadarorin Amurka, Kasashen yamamcin Turai da Sudan. Shine madugun kungiyar da ta kai farmakin 1 ga watan janairun 2008 kuma daya ne daga cikin mutane biyu da suka yi harbi. Bayan da ya arce daga kurkukun Khobar dake Khartoum a ran 11 ga watan Yunin 2010, Makawi ya koma da zama Somalia.