Labarin kan nasara

Mir Aimal Kansi

Wanda aka aiwatarda hukuncin kisa a kansa

Ran 5 ga watan janairu ne Mir imal Kansi ya kashe mutane biyu, ya lahanta wasu ukku har abada. Ba zato, ba tsammani ne, ba tareda wani ya tsokane shi ba, ya bude wuta da bindigarsa ta AK-47, ya soma harbin motocin dake tsate suna jira akan wata wutar titi, a gaban Hedkwatar Hukumar Leken Assirai ta Amurka ta CIA.

Jim kadan bayanda ya kai wannan harin, Kansi ya arce, ya fice Amurka kuma ya ci gaba da boyo har zuwa lokacinda aka cafke shi a Pakistan. Ran 10 ga watan Nuwamba na 1997 ne gungun masu yanke hukunci a wata kotu ta Fairfax, jihar Virginia, suka yanke hukunci akansa bayanda suka same shi da laifin kashe ma’aikatan CIA guda biyu.