Aikin Ta’addanci
Bayani akan ...

Harin Bama-bammai akan Barikin Sojan Kundumbaka

Lebanon | 23 ga watan Oktobar 1983

A ran 23 ga watan Oktobar 193 ne wani bam dake cikin mota ya tashi a barikin sojan kasashen Amurka da faransa dake cikin Rundunar Sojojin Kasa-da-Kasa dake Lebanon. Wannan harin ya hallaka daruruwan sojoji, ciki harda sojan kun dumbalan Amurka su 241. Daman wannan Rununar ta Kasa-da-Kasa bangare ce ta rtundunar kasashen duniya da aka kai Lebanon don suyi aikin kiyaye sulhu. Ana zargin cewa Hezbollah ce ta kitsa kai wannan harin tareda taimakon kayan aiki da kudade daga Iran.

Shirin Bada Tukuici Don Adalci na tayin bada tukuicin da ya kai har na Dala milyan 5 ga duk wanda ya bada bayanin da zai kai ga kama wadanda suka kai wannan harin.