Wanda ake nema
Bayani wanda zai kawo hukunci…

Mangal Bagh

Tukuicin Da Ya Kai Na Dala Milyan 3

Mangal Bagh shine shugaban Lashkar-e-Islam, wani ɓangaren ‘yan ta’adda wanda ke da alaƙa da Tehrik-e-Taliban Pakistan (TTP). Ƙungiyarsa na samun kuɗin shiga daga fataucin ƙwayoyi, fasa-ƙwauri, satar jama’a, hare-hare a kan Tawagar Ƙungiyar Tarayyar Turai, da kuma haraji a kan kasuwanci tsakanin Pakistan da Afghanistan.

Bagh ya jagoranci Lashkar-e-Islam tun 2006 kuma daga lokaci zuwa lokaci ya canza ƙawancensa domin kare kuɗaɗen shiga na haram a ƙarƙashinsu yayin da yake tilasta nau’in Musulunci na Deobandi Islam a yankunan gabacin Afghanistan da yammacin Pakistan waɗanda yake da iko da su musamman Gundumar Nangarhar, Afghanistan.

Wanda aka haifa a Hukumar Khyber, Pakistan, an yi Imani cewa ya na cikin tsakiyar shekarunsa na arba’in. Bagh ɗan ƙabilar Afridi ne. Yayi karatu a makarantun madrasa na shekaru masu dama kafin daga bisani ya yi faɗa tare da ƙungiyoyin sa kai a Afghanistan.

Karin Hotuna

Mangal Bagh