Wanda ake nema
Bayani wanda zai kawo hukunci…

Malik Abou Abdelkarim

Tukuicin Da Ya Kai Na Dala Milyan 3

Malik Abou Abdelkarim babba ne a cikin mayakan kungiyar ta’addanci ta al-Qaida dake Kasashen Islama na Maghreb (AQIM). A karkashin jgorancin Abdelkarim ne, kampaninsa ya sami makaman da aka yi anfani da su wajen sace-sacen mutane da yin aiyukkan ta’addanci kanana a kasashen Afrika ta Arewa da Afrika ta Yamma. Ana kyautata zaton Abdelkarim ne ya kashe wani dattijon Bafaranshe, dan shekaru saba’in da takwas, a Junhuriyar Nijer a watan Yulin 2010. Wani harin da kampanin Abdelkarim ya kai a watan Yunin 2010 ya haddasa mutuwar wasu sojan Algeria su 11.

Kungiyar al-Qaida a Kasashen Islama na Maghreb, wacce a can da aka sani da sunan Kungiyar Salafist ta Wa’azi da Yaki (GSPC) ta sha kai hare-haren ta’addanci a kasashen arewa-maso-yammacin Afrika. AQIM da kanta ta sha daukan alhakin kai hare-haren kunar bakin wake da sace-sacen mutanen Yammacin Turai, kashe-kashen gilla da kuma anfani da bama-baman gida.Ko a cikin watan Disambar 2007, kungiyar ta kai wasu hare-hare guda biyu lokaci guda akan Helkwatar wani shirin Majalisar Dinkin Duniya da kuma Majalisar Tsarin Mulki ta Algeria, inda mutane 42 suka hallaka, wasu 158 suka ji raunukka. Haka kuma AQIM ta dauki alhakin kisan gillar da aka yi a watan Yunin 2009 na dan Amurka Christopher Legget, wanda a lokacin yana Mauritania, ya na aikin ibada. A cikin watan satumbar 2012, AQIM ta umurci membobinta da su yi barazana ga Ma’aikatun jakadancin Amurka, kuma su kashe jakadun Amurka.

Ma’aikatar harakokin wajen Amurka ta kaddamarda kungiyar GSPC a matsayin Kungiyar ‘Yan ta’dda ta Kasashen waje a karkashin sashe na 219 na Dokar Shige da Fice da Zama Dan Kasa (kamar yadda aka gyara ta) ran 27 ga watan Maris na 2002, ta kuma kara sabunta wannan kaddamarwar da aka yi wa kungiyar a karkashinsabon sunanta na AQIM ran 16 ga watan Oktoba, 2009. Ma’aikatar Baitulmalin Amurka kuma ta kaddamarda kungiyar a matsayin Kungiyar ta’adda ta Musamman a karkashin Dokar Hukuma mai lamba 13224 ta ran 21 ga watan Febrariu, 2008.