Wanda ake nema
Bayani wanda zai kawo hukunci…

Maalim Salman

Tukuicin Da Ya Kai Na Dala Milyan 3

Marigayin shugaban al-Shabaab Ahmed Abdi aw-Mohamed (Godane) ne ya zaɓi Maalim Salman ya zama shugaban masu yaki da ƙasashen waje na Afrika ɗin al-Shabaab. Ya yi horon masu aikin al-Shabaab wanda ba ɗan Somali ne su ba kuma ya kasance cikin wanda su ke aiki cikin Afrika kuma manufan su shi ne su kai hari wajen masu yin yawon bude ido, kamfanonin nishaɗi, da kuma majami’un krista.

Duk da suna yin yawan aikin su a waje da Somalia, an san cewa Salman yana zaman shi a cikin Somalia in da ya ke horar masu yakin ƙasar waje cikin Somalia kafin ya raba su zuwa wani wurin aiki. Cikin wasu harin ‘yan ta’adda da ya kai, al-Shabaab ne da alhakin harin da an kai wajen Babban Ma’aikatar Kasuwanci mai sunan Westgate a cikin Nairobi, ƙasar Kenya, wanda ya kashe mutane adadin su har zuwa sitin da biyar.