Aikin Ta’addanci
Bayani akan ...

Hare-haren Bam na Wasiku

Daga Disambar 1996 zuwa ga Janairun 1997

A tsakanin wattanin Disambar 1996 ne da Janairun 1997 aka aika wasu bama-bammai a cikin siffar wasikun taya murnar rannakun hutu zuwa ta gidajen waya zuwa mutane daban-daban dake a Amurka da Ingila.

Daga cikin wadanan bama-baman na wasiku, 13 an karbe su ne a opisoshin jaridar Al Hayat dake biranen New York, Washington, DC da kuma Lomdon. Daya daga cikin bama-baman ya fashe a London, inda ya ji wa mutane biyu munanan raunukka. Sauran bama-baman ukku kuma an gano su ne a Amurka, a wani gidan kurkuku na tarayya dake garin Leavenworth.

Kowane daga cikin bama-bamman nan yana dauke da hatimin kan sarkin da aka buga a ran 21 ga watan Disambar 1996 a Alexandria ta Masar., kuma daga cikinsu ba wanda ke dauke da adereshin wanda ya aiko su. Bama-baman sun zo ne a cikin farin ambulon wanda aka yi anfani da shirytayyun rubuce-rubuce na komputa da sauran alamomi.

Shirin Bada Tukuici Don Adalci na tayin bada tukuicin da ya kai har na Dala milyan 5 ga duk wanda ya bada bayanin da zai kai ga kama wadanda suka kai wannan harin.

Karin Hotuna

Hare-haren Bam na Wasiku