Aikin Ta’addanci
Bayani akan ...

Sace-Sace da Kashe-kashen da aka yi

Lebanon | daga shekarar 1985 zuwa 1989

Sace-sacen mutane da kashe-kashen gilla bangare ne na rikicin yin garkuwan da aka yi da mutane a Lebanon na tsawon shekaru goma da ‘yan ta’addar Hezbollah suka gudanar. Wannan rikicin garkuwar an yi shine tsakanin shekarar 1982 zuwa 1992.

A ran 16 ga watan Maris na shekarar 1984 ne ‘yan ta’adda suka sace shugaban Opishin CIA na Beirut, William Buckley. An yi wa Buckley tambayoyi, aka gana mishi azaba kuma aka tsare shi har na tsawon wattani 15 kafin a kashe shi.

A ranar 3 ga watan Disambar 1984 ne aka bada sanarwar cewa jami’in kula da dakin Karatu na Beirut Peter Kilbum ya bace. Wattani goma sha shidda bayan haka ne aka bindige kuma aka kashe shi, tareda wasu mutane biyu da aka kama su tare, sannan aka yi jifa da gawwakinsu a cikin wasu tsaunukka na gabashin Beirut.

ran 17 ga watan Fabrairun 1988 ne aaka yi awon gaba da Kanar William Higgins daga cikin motarsa ta aiki mallakar Sojan Kiyaye Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya. A matsayin wanda ake garkuwa da shi, an yi wa Kanar Higgins tambayoyi, aka gana mishi azaba kafin a kashe shi. Sai dai ba’a tabattarda ranar da aka kashe shi din ba.

Shirin Bada Tukuici Don Adalci na tayin bada tukuicin da ya kai har na Dala milyan 5 ga duk wanda ya bada bayanin da zai kai ga kama wadanda suka kai wannan harin.

Wadanda abin ya shafa

Hoton William Higgins
An kashe William Higgins 1989
Hoton Peter Kilburn
An kashe Peter Kilburn 1986
Hoton William Buckley
An kashe William Buckley 1985