Aikin Ta’addanci
Bayani akan ...

Harin Bam kan Ginin Khobar

Dhahran, Saudi Arabia | 5 ga Yuni, 1986

A raar 25 ga watan Yunin 1996 ne ‘yan kungiyar Saudi Hizballah suka kai harin taaddancin akan Gidajen Khobar dake kusa da Dhahran, Saudi Arabia. A wannan lokacin, sojojin Amurka na zaune a cikin wadanan gidaje. ‘Yan ta’addar sun tuka wata mot ace da aka shake da nakiyoyi, suka fasa ta, suka nakkasa ta kwata-kwata illa wani gine da yafi kusa da ita. Wannan farmakin ya hallaka sojojin Amurka 19 da wani dan kasar Saudi Arabia daya; ya kuma raunana mutane 372 daga kasashen duniya daba-daban.

A ran 21 ga watan Yunin 2011 ne mahukunta a kotun tarayya ta Alexandria suka sami ‘yan ta’adda 14 da laifin kai wannan harin. Wannan zargin ya tuhumci Ahmad al-Mughassil, Ali el-Hoorie, Ibrahim al-Yacoub, Abdelkarim al-Nasser da wasu da dama da laifukka barkatai. A karshin hukuncin, ab sami tara daga cikin ‘ytan ta’addar 14 da laifin aikata laifukka 46 iri-iri da suka hada da wadanan: kulla makircin Amurkwa sa ma’aikatan Gwamnatin Tarayya ta Amurka; anfani da makaman kare dangi da kuma laifin nakkasa kadarorin Amurka.

Shirin Bada Tukuici Don Adalci na tayin bada tukuicin da ya kai har na Dala milyan 5 ga duk wanda ya bada bayanin da zai kai ga kama wadanda suka kai wannan harin.