Wanda ake nema
Bayani wanda zai kawo hukunci…

Khalil Haqqani

Tukuicin Da Ya Kai Na Dala Milyan 5

A matsayinshi na zaman kusar Kungiyar Haqqani, Khalil al-Rahman Haqqani yana tara wa Taliban kudade, yana kuma taimakawa wajen gudanarda aiyukkan Taliban a Afghanistan. Tun shekarar 2010 ya soma Tara wa mayakan Taliban kudade a Lardin Logar, Afghanistan. A shekarar 2009, Khalil na cikin mutane da dama dake da alhakin tsare fursunonin yaki da kungiyoyin Taliban da Haqqani suke kamawa, suna tsarewa. Khalil yana karban umurni ne daga wajen Bappansa, Sirajuddin Haqqani wanda tun watan Maris na shekarar 2008 Amurka ta kaddamarda shi (a matsayin Dan Ta’adda) a karkashin Dokar Hukuma mai lamba 13224. Ana kuma alakanta Khalil da yin aiki da sunan al-Qaida, da aiyukan yake-yake na al-Qaida din. A shekarar 2002 ne ya rinka aika mayaka don karfafa rundunonin al-Qaida dake a Lardin Paktia na Afghanistan.

A ran 9 ga watan Fabrariun 2011 ne Ma’aikatar Harakokin Wajen Amurka ta kaddamarda Khalil al-Rahman Haqqani a matsayin Rikakken Dan Ta’adda na Duniya a karkashin Dokar Hukuma mai lamba 13224.

Karin Hotuna

Karin Hoton Khalil Haqqani
Karin Hoton Khalil Haqqani